Inah Lucas: Mace Mafi Tsufa a Duniya Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Tana da Shekaru 116
- Mai riƙe da kambun mace mafi tsufa a duniya, Inah Canabarro Lucas ta mutu tana da shekaru 116 da haihuwa a ban kasa
- Lucas ta mutu ne a garin Porto Alegre da ke ƙasar Brazil watanni ƙalilan bayan ta karɓi kambun mace mafi tsufa a duniya
- An ruwaito cewa bayan rasuwarta, kambun ya koma hannun Ethel Caterham mai shekaru 115 daga Surrey a ƙasar Ingila
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Brazil - Matar da ke riƙe da kambun mace mafi tsufa a duniya, wata ƴar ƙasar Brazil mai suna Inah Lucas ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 116 da haihuwa.
Rahotanni sun nuna cewa Inah Lucas ta mutu ne watanni kadan bayan ta karbi kambun girmamawa na mafi tsufa a duniya.

Asali: Twitter
Guinness World Record mai ba da kambun bajinta na duniya ta tabbatar da rasuwar matar a shafinta na X ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mace mafi tsufa a duniya ta mutu a Brazil
Lucas ta rasu ne a Porto Alegre, Brazil, kuma Kungiyar Teresian Sisters, masu yi wa coci hidima ta bayyana godiya “ga sadaukarwa da jajircewar” da ta nuna a tsawon rayuwarta.
An haifi Lucas a ranar 8 ga Yuni, 1908, kuma ta zama mafi tsufa a duniya ne a watan Janairu, 2025 bayan rasuwar Itooka Tomiko, 'yar Japan wadda ita ma tana da shekaru 116.
Ta zama baiwar Allah, mai hidima a wuraren bauta a shekara ta 1934 tana ƴar shekaru 26, a lokacin da duniya ke tsakanin yakin duniya na farko da na biyu.
Hasashen masana kan rayuwar Inah Lucas
Rayuwarta ta jawo hankalin masana tarihin tsawon rai da al’ummomin addini. LongeviQuest ta bayyana cewa an haife ta da rauni, kuma aka ce ba za ta daɗe a duniya ba.
Duk da hakan, Inah Lucas ta rayu fiye da karni guda, kuma ta rika danganta tsawon rayuwarta da imani da Allah.
A 2018, lokacin da ta cika shekaru 110, ta samu albarkar Fafaroma Francis, wanda shi ma ya rasu a makon da ya gabata yana da shekaru 88.
Duk da cewa Inah Lucas ta dinga cewa an haife ta a ranar 27 ga Mayu, 1908, amma masu bincike sun tabbatar da cewa ranar haihuwarta ita ce 8 ga Yuni, 1908.
Kungiyar LongeviQuest ta ce Lucas ita ce ta 15 mafi tsufa da aka tabbatar a tarihin dan Adam, kuma ita ce bazawara ta biyu mafi tsufa bayan Lucile Randon, ƴar Faransa, wacce ta rasu tana da shekaru 118 a 2023.
Bayan rasuwarta, Ethel Caterham mai shekaru 115 daga Surrey, Ingila, ita ce yanzu mafi tsufa a duniya, a cewar LongeviQuest da Gerontology Research Group (GRG).
Namiji mafi tsufa a duniya ya mutu
A baya, mun kawo maku cewa mutumin da ya fi kowane namiji tsufa a duniya, dan asalin ƙasar Birtaniya John Tinniswood, ya mutu yana da shekara 112.
A wata sanarwa da suka fitar, iyalansa sun tabbatar da cewa ɗan uwansu ya cika cikin farin ciki, kewaye da kida da ƙauna a ranarsa ta karshe a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng