Lokaci Ya Yi: Mutumin da Ya Fi Kowa Tsufa a Duniya Ya Mutu Yana da Shekara 112

Lokaci Ya Yi: Mutumin da Ya Fi Kowa Tsufa a Duniya Ya Mutu Yana da Shekara 112

  • Mutum mafi tsufa a duniya ɗan ƙasar Birtaniya, John Tinniswood ya mutu yana da hekara 112 ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024
  • Iyalansa sun tabbatar da cewa ɗan uwansu ya cika cikin farin ciki, kewaye da kida da ƙauna a ranarsa ta karshe a duniya
  • Mutumin dai ya shiga kundin gwaninta na duniya watau Guinness World Records a watan Afrilu bayan wani ɗan kasar Venezuela

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United Kingdom - Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya, dan asalin ƙasar Birtaniya John Tinniswood, ya mutu yana da shekara 112.

An haifi Tinniswood a Liverpool a ranar 26 ga Agusta, 1912, kuma ya mutu ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024.

John Tinniswood.
Mutum mafi tsufa a duniya ɗan salin ƙasar Birtaniyaya mutu yana da shekara 112 Hoto: @GWR
Asali: Twitter

Kundin gwaninta 'Guinness World Records' mai tattara bayanan tarihi a duniya ya tabbatar da mutuwar mutumin a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Babu yadda za a yi shugabancin Najeriya ya dawo hannun mutanen Aewa," Okupe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum mafi tsufa a duniya ya mutu a Ingila

Ya zama mutum mafi tsufa a duniya a watan Afrilu bayan mutuwar Juan Vicente Perez dan kasar Venezuela mai shekaru 114.

"Yana kewaye da kida da ƙauna a ranarsa ta ƙarshe duniya," in ji danginsa a cikin wata sanarwa da suka fitar.

Iyalan marigayin sun godewa dukkan waɗanda suka nuna kulawarsu a kan John Tinniswood a lokacin rayuwarsa.

Marigayin ya ba al'ummar duniya shawara

A lokacin rayuwarsa, Tinniswood ya shaida wa kundin gwaninta Guinness World Records cewa sirrin daɗewarsa a duniya shi ne "sa'a mai kyau."

"Ko ka yi tsawoncin kwana ko akasin haka, ba a hannun mu yake ba, ba abin da mutum zai iya yi game da kwanakinsa aduniya," in ji shi.

Sai dai ya bai wa al'ummar wannan zamanin shawarar cewa su riƙa daidaita komai na rayuwa domin zama cikin ƙoshin lafiya.

Sarki mafi daɗewa a sarauta ya rasu

Kara karanta wannan

Badakalar N110bn: Yahaya Bello ya tattaro tawagar lauyoyi, ya dura ofishin EFCC

A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya yi wa sarkin Beli da ke yankin ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi, Muhammadu Inuwa rasuwa yana da shekara 111.

Basaraken wanda ya shafe shekara 91 a kan sarauta shi ne sarki mafi daɗewa a kan karagar mulki, ya rasu a asibitin FMC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262