Kiristoci Sun Fusata, Sun Yi Allah Wadai da Trump kan Sanya Kayan Fafaroma
- Shugaban Amurka Donald Trump ya jawo abin surutu bayan wallafa wani hoto da na’ura ta kirkira wanda ya nuna shi cikin kayan Fafaroma
- Limaman Katolikan New York sun zargi Trump da wulakanta addini, suna cewa hoton ya zo a daidai lokacin da ake shirin zaben sabon Fafaroma
- Fadar White House ta musanta cewa Trump ya yi ba'a da manufar raina mukamin Fafaroma, ta ce Shugaban ya halarci jana’izarsa a Vatican
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake jefa kansa cikin ce-ce-ku-ce bayan wallafa wani hoto da na’ura ta kirkira da ke nuna shi sanye da kayan Fafaroma.
Hoton da aka wallafa a dandalin sada zumunta na Fadar White House a ranar Juma’a da daddare, ya zo ne a daidai lokacin da mabiya Katolika ke cikin jimamin rasuwar Fafaroma Francis.

Asali: Getty Images
BBC ta rahoto cewa kungiyar limaman Katolika ta jihar New York ta bayyana rashin jin daɗinta da wallafa hoton.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Limaman cocin sun bayyana cewa hakan cin mutunci ne da raina addini, musamman ganin cewa ana shirin gudanar da zaɓen sabon Fafaroma a mako mai zuwa.
Kiristoci sun yi Allah-wadai da Donald Trump
A cikin hoton da aka wallafa, an ga Trump sanye da farar riga irin ta limamai da hular Fafaroma, ya daga yatsarsa sama cikin wani irin salo na girmamawa.
CNN ta rahoto cewa kungiyar malaman addinin Kirista a New York ta yi Allah-wadai da wannan hoto tana mai cewa:
"Babu wani abin dariya ko hikima a wannan hoto.
"Muna jimamin birne masoyinmu Fafaroma Francis, kuma manyan limamai na shirin fara zaɓen sabon jagora. Kada ka raina mu."
Haka kuma, tsohon Firaministan Italiya, Matteo Renzi ya caccaki Trump bisa wallafa hoton, yana mai cewa:
"Wannan hoto cin mutunci ne ga masu imani da addini."
Fadar White House ta kare Trump daga suka
Sai dai Fadar White House ta musanta zargin cewa Trump yana raina addini ko mukamin Fafaroma.
Mai magana da yawun fadar, Karoline Leavitt, ta ce:
"Shugaba Trump ya je har Italiya domin halartar jana’izar Fafaroma Francis kuma yana daya daga cikin masu kare addini da 'yancin mabiya Katolika a duniya."

Asali: Getty Images
Sai dai duk da haka shugaban Katolika na New York, Timothy Dolan, wanda ke da kusanci da Trump, ya bayyana rashin jin dadinsa game da da hoton.
Timothy Dolan ya ce:
“Ba daidai bane hakan, ina fata Trump ba shi da hannu wajen kirkirar hoton,”
Da aka tambaye shi ko ya kamata White House ta goge hoton ko ta nemi afuwa, sai ya ce cikin Italiyanci "Ya rage nasu", ya ƙi ƙara magana kan batun.
Trump ya cire hoton Obama a White House
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya cire hoton Barrack Obama a fadar White House.
Rahotanni sun nuna cewa Donald Trump ya maye hoton Obama da wani zane da aka masa a lokacin da aka harbe shi.
Bayan cire hoton da Donald Trump ya yi, mutanen Amurka da sauran yankunan duniya sun caccake shi suna cewa hakan bai dace ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng