Amurka ta nunawa duniya cikakkiyar hujja cewa Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makamai
- Bayan kowanne hari dai, Amurka kan dauki samurin burunguzai da makamai da aka harba a Yemen
- Amurkar kuma ita ta sayarwa da Saudiyya makamai da itama take kai hari dasu Yemen
- Iran ta dade tana mikawa masu tawaye a kasashen duniya makamai
A bayan kisan da 'yan tawayen Houthi suka yi wa Abdalla Saleh, tsohon abokinsu kuma tsohon shugaban kasar ta Yemen, wanda hargitsin son juyin juya hali ya rutsa da, a 2011, Amurka ta matsa kaimi wajen ganin duniya ta dauki mataki kan Houthi din.
Su dai Houthi, 'yan Shi'a ne da suka kwace ikon mulki daga masu mulki 'yan sunni a Yemen, kudu da Saudiyya, shaqa da masarautar Saudiyya bata so, ace kasashen shi'a sun kewaye ta, gabas da kudu da arewa.
DUBA WANNAN: A bana za'a kammala sayar da 9mobile
Amurka, mai goyon bayan Saudiyyar ta bata makaman hari kan Yemen din, su kuma Houthi, sun sami goyon bayan Iran. Sai kuma yanzu Nikki Haley tayi holin makamai da Houthi din ke amfani dasu a kasar ta Yemen, wanda tace, dukkan hujja ta nuna daga Iran aka fito dasu.
Iran dai ta dade tana rabawa masu tada kayar baya makamai, a kasashe daban daban, kamar su Lebanon, da Syria, da Iraki, kai har ma da Najeriya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng