Sanusi II Ya Halarci Nadin Sabon Khalifan Tijjaniyya a Kasar Burkina Faso

Sanusi II Ya Halarci Nadin Sabon Khalifan Tijjaniyya a Kasar Burkina Faso

  • Mai Martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, ya halarci taron nadin Khalifan Tijjaniyya da aka gudanar a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso
  • Taron ya samu halartar ministocin ƙasar da sauran manyan jami’ai, inda Sanusi II ya tattauna da Mataimakin Shugaban Ƙasar bayan taron
  • Kafin tafiyarsa, Sanusi ya karɓi bakuncin Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, wanda su ke da kusanci tun daga lokacin da su ke aiki a harkar banki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II, ya kasance cikin manyan baki da suka halarci babban taron Darikar Tijjaniyya a kasar Burkina Faso.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi nadin sabon Khalifan Tijjaniyya a ƙasar Burkina Faso a ranar Lahadi, 4 ga Mayu, 2025.

Sanusi Ii
Sanusi II ya halarci taron nadin Khalifan Tijjaniyya a Burkina Faso. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da masarautar Kano ta wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da aka gudanar a birnin Ouagadougou, ya jawo manyan mutane daga sassa daban-daban ciki har da ministocin ƙasar da jami’an tsaro da shugabannin addini.

Muhammadu Sanusi II ya je nadin Khalifan Tijjaniyya

A matsayin daya daga cikin fitattun shugabannin addini da masarauta a Najeriya da Afirka, Sanusi II ya samu gayyata zuwa taron nadin sabon Khalifan Tijjaniyya a Burkina Faso.

Taron nadin Khalifan ya gudana cikin lumana da tarbar mutunci, inda manyan jami’an gwamnati suka halarta.

Ciki manyan baki har da ministan cikin gidan Burkina Faso, M. Zerbo; Ministan Tsaro Umarou Yabe.

Haka zalika Ministan Tattalin Arziki da Harkokin Kudi Dr Abubakar Nakalbo da shugaban rundunar 'yan sanda ta ƙasar, Dr. Mahadou Sana sun halarci taron.

Sanusi
Sanusi da baki bayan nadin Khalifan Tijjaniyya a Burkina Faso. Hoto: Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

An yaba da rawar da Sanusi II ke takawa wajen hada kan musulmi da kuma kokarinsa na yada ilimin addini da ci gaban al’umma.

Sanusi II ya gana da mataimakin shugaban kasa

Bayan taron nadin Khalifa, Sarkin Sanusi II ya gana da Mataimakin Shugaban Ƙasar Burkina Faso domin tattauna hanyoyin hadin gwiwa a fannin addini da zamantakewa.

Wannan ganawa na daga cikin yunkurin Sanusi II na kara kyautata dangantaka tsakanin masarautar Kano da sauran kasashen musulmi, musamman a nahiyar Afirka.

Sarki Sanusi II ya karbi bakuncin gwamna Otti

Kafin tafiyarsa Burkina Faso, a ranar Juma’a, 2 ga Mayu, 2025, martaba Muhammadu Sanusi II ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, a fadarsa da ke Kano.

Alex Otti, wanda tsohon babban darakta ne a bankin Diamond, ya kasance mai kusanci da Sanusi II tun lokacin da dukkansu ke aiki a fannin hada-hadar kudi.

Ana kallon wannan ganawa a matsayin sabuwar hanya ta musayar ra’ayi da karfafa hadin kai tsakanin shugabannin siyasa da na masarauta a Najeriya.

El-Rufa'i ya ziyarci sarki Sanusi II a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya ziyarci Muhammadu Sansui II a Kano.

Yayin ziyarar, an hango Nasir El-Rufa'i da dan shi cikin wata tawaga da ta mara masa baya zuwa fadar Sanusi II.

El-Rufa'i ya yi magana kan harkokin shugabanci a Najeriya da muhimmancin zaben shugabanni na gari a zaben 2027 mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng