'Ina Sanusi II?': An Tambayi Me Ya Hana Sarki Zuwa Taro da Aminu Ado a Kaduna

'Ina Sanusi II?': An Tambayi Me Ya Hana Sarki Zuwa Taro da Aminu Ado a Kaduna

  • Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya halarci taron sarakunan Arewa da aka gudanar a birnin Kaduna a ranar Asabar, 26 ga watan Afrilu, 2025
  • Masarautar Kano ta wallafa hotunan ganawar tsakanin Sarki Aminu Ado Bayero da Gwamna Uba Sani a shafinta na manhajar X a jiya
  • Sanarwar ta bayyana cewa Sarki Aminu Ado Bayero na daga cikin manyan sarakunan da suka gana da Gwamnan Kaduna a wani taro
  • Halin da aka gani na rashin halartar Muhammadu Sanusi II ya janyo tambayoyi, inda jama'a suka ce taron sarakunan Arewa amma bai ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya halarci taron sarakunan gargajiya na Arewa da aka gudanar a Kaduna.

Basaraken ya samu halartar taron a jiya Asabar 26 ga watan Afrilun 2025 a birnin Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Aminu Ado ya halarci taron sarakunan gargajiya a Kaduna
Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi hawa a Kano yayin da Aminu Ado ya je Kaduna taron sarakuna. Hoto: Sanusi Dynasty II, Masarautar Kano.
Asali: Twitter

Shafin Masarautar Kano shi ya wallafa haka tare da hotunan ganawar sarakunan da Gwamna Uba Sani a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Sanusi II ya yi hawan Babban Daki

Wannan na zuwa ne yayin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gudanar da Hawan Babban Daki a jiya Asabar bayan dawowarsa daga birnin London.

Masu sharhi da magoya baya sun yi addu’o’in fatan alheri ga Sarki Sanusi II domin Allah ya sa a yi taron lafiya ba tare da tashin hankali ba kafin fara hawan.

A gefe guda kuma, ana shirin bikin, Sarki Aminu Ado Bayero ya halarci wani taro tare da wasu sarakunan Arewa a Kaduna bayan dawowa daga Umrah.

Aminu Ado ya halarci taron sarakuna a Kaduna

A cikin sanarwar, aka ce Aminu Ado Bayero na daga cikin sarakuna da suka sanya labule da Gwamna Uba Sani.

Sanarwar ta ce:

"Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gana da Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, tare da sauran Sarakunan gargajiya na Arewa a wata ganawar sirri da suka yi.

"Allah ya taimaki Sarki ya tsawaita zamani."
Aminu Ado Bayero ya samu halartar taron sarakuna a Kaduna
Sarki Sanusi II ya yi hawa a Kano yayin da Aminu Ado ya halarci taron sarakuna a Kaduna. Hoto: Masarautar Kano, Sanusi II Dynasty.
Asali: Twitter

Taron Kaduna: Wasu sun taso Sanusi II a gaba

Sai dai hakan ya jawo maganganu duba da cewa ba a gano Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ba.

Mafi yawan masu magana sun yi tambayar dalilin rashin halartar Sarkin duba da taro ne na sarakunan gargajiya a Arewa.

Wani mai amfani da X, @Ahmad_Gogel ya ce ana can ana taro a Kaduna amma bai ga Mai Martaba ba.

A rubutunsa ya ce:

Ana can Kaduna ana taron Sarakuna, wani kuma yana Kano an bar shi da hawa raƙumi"

Mutane da yawa sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan rubutu yayin da wasu ke taɓa Sarki Sanusi II wasu ko shaguɓe suke wa Aminu Ado Bayero.

Aminu Ado Bayero ya yabawa mulkin Tinubu

A baya, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa kafa hukumar raya kiwo da makiyaya ta kasa.

Basaraken ya ce wannan mataki zai kawo ci gaba da zaman lafiya a Arewacin Najeriya da ma sauran yankuna.

Sarkin ya jinjinawa Farfesa Attahiru Jega da Dr. Abdullahi Umar Ganduje domin jagorantar kwamitin hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.