Sarki Sanusi II zai Jagoranci Gagarumin Bikin Nadin Sarautar Yariman Kano

Sarki Sanusi II zai Jagoranci Gagarumin Bikin Nadin Sarautar Yariman Kano

  • Za a gudanar da nadin sabon Yariman Kano, Alhaji Ahmed Abbas Sanusi a fadar Sarkin Kano ranar Juma’a mai zuwa
  • An ruwaito cewa sabon Yariman Kano ya kasance Wakilin Marigayi Galadima, wanda ya rasu kwanan nan bayan jinya
  • Hakan na zuwa ne bayan sarki Muhammadu Sanusi II ya yi sababbin nade-nade da sauye-sauye a majalisar masarautar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Masarautar Kano za ta gudanar da nadin sabon Yariman Kano, Alhaji Ahmed Abbas Sanusi.

Za a yi nadin sarautar ne a wani babban biki da za a yi a fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu ranar Juma’a, 2 ga watan Mayu.

Sanusi II
Za a yi nadin Yariman Kano ranar Juma'a. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan nadin sarautar ne a cikin wani sako da fadar mai martaba Sanusi II ta wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin na zuwa ne bayan rasuwar Marigayi Galadiman Kano, Abbas Sanusi, inda Alhaji Ahmed Abbas Sanusi ya kasance wakilinsa kafin rasuwarsa.

Masarautar ta bayyana cewa wannan nadin wani bangare ne na cike guraben da suka bulla a tsarin masarauta.

Masarauta ta tabbatar da ranar nadin Yarima

Sanarwar masarautar ta tabbatar da cewa za a yi nadin Alhaji Ahmed Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano a ranar Juma’a mai zuwa a fadar Kofar Kudu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a gudanar da bikin nadin Yariman ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Bayanai sun nuna cewa bikin na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da tsarin gado da sarauta a masarautar.

Ahmed Abbas Sanusi, wanda ya kasance wakilin Marigayi Galadiman Kano kafin rasuwarsa, na cikin manyan masarautar da ake sa ran za su taka rawa wajen tafiyar da harkokin sarauta.

Nade-naden da Sanusi II ya yi a baya

A kwanakin baya Sarki Sanusi II ya amince da nadin Alhaji Munir Sanusi Bayero daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano.

Masarautar Kano ta tabbatar da cewa an mayar da Alhaji Kabiru Tijjani Hashim daga Turakin Kano zuwa Wamban Kano.

Haka nan, Alhaji Mahmud Ado Bayero daga Tafidan Kano ya koma Turakin Kano, sannan Adam Lamido Sanusi (Ashraf) ya zama sabon Tafidan Kano.

Masarautar ta bayyana cewa wadannan nade-nade na daga cikin tsarin sabunta jagoranci da tafiyar da harkokin masarauta.

Sarki Sanusi II ya halarci taro a Legas

A gefe guda, Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya halarci wani taro na murnar cika shekara 20 na kamfanin Chapel Hill Denham a Legas a ranar Litinin 28 ga Afrilu.

Taron ya samu halartar Ministan Kudi na ƙasa, Wale Edun, Gwamnan Jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu.

Sanusi II
Sanusi II ya halarci taro a Legas. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Shugaban Bankin Africa (AfDB) Akinwumi Adesina da Shugaban Chapel Hill Denham, Bolaji Balogun da sauran manyan baki sun halarci taron.

Sanusi II ya yi hawan babban daki a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya jagoranci Hawan Babban Daki a jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan sarkin ya dawo daga wata ziyara ta musamman da ya kai birnin London na kasar Birtaniya.

Legit ta rahoto cewa an shirya cewa sarki Muhammadu Sanusi II zai yi hawan ne a kan rakumi kamar yadda al'adar ranar ta tanada.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng