Ana Hada Rigakafin Maciji daga Jinin Mutumin da Macizai 200 Suka Ciza

Ana Hada Rigakafin Maciji daga Jinin Mutumin da Macizai 200 Suka Ciza

  • Wani tsohon direban mota a Amurka da ya sha gubar macizai tsawon shekaru 18 na iya zama tushen rigakafin kowanne irin cizon maciji
  • Masana sun tabbatar da cewa gubar da Tim Friede ke sha ta taimaka wajen gina kariya daga nau’ukan guba masu hadari da ke kashe mutane
  • Sabon binciken da aka gudanar ya nuna cewa akwai yiwuwar samar da rigakafin da zai yi aiki ba tare da bambanta nau’in cizon maciji ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Masana kimiyya sun gano wata gagarumar dama a fannin lafiya daga wani mutum dan kasar Amurka, Tim Friede, wanda ya shafe fiye da shekaru 18 yana shan gubar macizai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tim Friede ya shafe shekaru yana shan gubar ne domin ya kare jikinsa daga cizon maciji.

Maciji
Mutumin da ya sha saran maciji sama da sau 200. Hoto: @AkashVerma_IFS
Asali: Twitter

Rahoton New York Times ya nuna cewa Friede ya ce ya fara wannan aikin ne domin kare kansa yayin da yake kula da macizai, amma daga baya ya juya hakan zuwa wani abu na daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce daga baya ya sadaukar da aikin domin taimakon sauran mutane da cizon maciji ke kashewa a duniya.

Bincike ya nuna cewa jinin Tim Friede yana dauke da sinadarai masu kariya daga gubar macizai iri-iri.

Binciken samar da rigakafin cizon maciji

Rigakafin cizon maciji na yanzu na bukatar daidaituwa da nau’in gubar macijin da ya yi cizo, domin kowanne irin maciji yana da nau’in guba daban.

Amma masu bincike daga kamfanin kimiyya na Centivax da ke Amurka sun fara neman sinadaran da za a iya aiki da su wajen magance kowace irin gubar maciji.

Shugaban kamfanin, Dr Jacob Glanville, ya ce a lokacin da ya samu labarin Tim Friede, ya fahimci cewa yana da irin sinadaran da suke nema.

Dr Jacob Glanville ya ce:

“Na kira shi na ce ‘zan so in samu jininka domin yin bincike da shi.”

Friede ya sha cizon maciji sau 200

Friede ya ce ya sha guba fiye da sau 700 tare da cizon macizai fiye da sau 200, har ma sau biyu cizon maciji kobra ya sa shi kwanciya a gadon asibiti rai a hannun Allah.

BBC ta rahoto cewa masana sun ce jininsa ya bayar da dama wajen kirkirar rigakafi da za a iya amfani da shi a duk duniya, ba tare da la’akari da nau’in maciji ba.

Macikji
Ana fatan samar da rigakafin cizon maciji na bai daya a duniya. Hoto: Getty Image
Asali: Twitter

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike a kan jinin Friede tare da fatan zai samar da mafita ga cizon maciji wanda ke ci gaba da zama barazana ga rayukan dubban mutane a duniya.

Maciji ya kashe sojan Najeriya a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wata jami'ar soja a Najeriya ta rasa ranta a sanadiyyar cizon majici a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta shiga bandaki ne domin biyan bukata sai ta hadu da tsautsayin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mummunan lamarin ya faru da jami'ar sojan ne a wani barikin sojojin saman Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng