Zance Ya Kare, Majalisun Dokokin Jihohi 36 Sun Mika Matsayarsu kan Kafa Yan Sandan Jihohi
- Majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar domin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi
- Amincewar ta samu kashi 100 cikin 100, inda ta zarce adadin jihohi 24 da kundin tsarin mulki ya tanada
- Rahotanni sun nuna cewa yanzu an kammala tantance ƙudirin, kuma ana shirin miƙa shi ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Dukkan majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya sun amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar domin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi.
Magatakardar Majalisar Dokokin Tarayya, Kamoru Ogunlana, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, inda ya ce amincewar ta nuna cewa dukkan majalisun dokokin jihohin sun goyi bayan ƙudirin.

Source: Twitter
A rahoton Daily Trust, ya bayyana cewa amincewar ta zarce sharadin kundin tsarin mulki na samun goyon bayan aƙalla majalisun dokokin jihohi 24, kamar yadda sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya tanada.

Kara karanta wannan
"Majalisun dokoki na jihohi 4 ba su mika matsayarsu kan kafa 'yan sandan jiha ba"
Abin da ƙudirin ya ƙunsa
Ƙudirin mai taken A Bill for an Act to Alter the Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 to Provide for the Establishment of State Police Services and for Related Matters, na neman samar da tsarin doka wanda zai ba da damar kafa rundunonin ’yan sandan jihohi.
Ogunlana ya ce a baya ƙudirin ya cika dukkan buƙatun kundin tsarin mulki da na gudanarwa da ake bukata kafin a miƙa shi.
Sai dai shugabannin Majalisar Dokokin Tarayya sun bayar da umarnin ɗan jinkiri domin ba wa ƙasar damar samun cikakkiyar fahimtar juna tare da tuntubar dukkan jihohi.
Ya ce yanzu ofishinsa ya kammala tantancewar, abin da ya buɗe hanyar miƙa ƙudirin ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya hannu.
Martanin magatakardar majalisa
Magatakardar ya bayyana amincewar da dukkan jihohin suka yi a matsayin wata alama ta haɗin kai tsakanin Majalisar Dokokin Tarayya da majalisun dokokin jihohi.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027
Ya kuma ce hakan ya nuna haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin zartarwa na gwamnati a matakin tarayya da na jihohi.
Ogunlana ya ƙara da cewa wannan mataki zai bude dama ga Majalisar Dokokin Tarayya wajen miƙa wasu ƙudirorin gyaran kundin tsarin mulki ga majalisun dokokin jihohi domin su duba su.
Ya yaba wa gwamnonin jihohi 36, shugabannin majalisun dokokin jihohi da mambobinsu, da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kan da suka bayar yayin gudanar da aikin gyaran kundin tsarin mulkin.

Source: Twitter
Dalilin neman ’yan sandan jihohi
Shirin kafa rundunonin ’yan sandan jihohi na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na sake fasalin tsarin aikin ’yan sanda a Najeriya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a ƙasar, tare da kiraye-kirayen a rab ikon gudanar da aikin ’yan sanda domin bai wa jihohi damar taka rawa sosai wajen tabbatar da tsaro.
Matakin da Majalisar dattawa take kai
A baya kun ji cewa Majalisar tarayya na dakon rahoton matsayar majalisun dokokin jihohi hudu, wadanda ba su mika matssyarsu a hukumance ba.
Shugaban Masu rinjaye na Majalisar dattawa, Sanata Bamidele, wanda ke wakiltar mazaɓar Sanatan Ekiti ta Tsakiya, ya ce duk da ana ci gaba da jiran rahotannin jihohin huɗun, rashin aika su ba zai hana ’yan majalisar tarayya ci gaba da aikin ba.
Asali: Legit.ng