Babu karanci maganin cizon maciji a Najeriya – Ministar kula da kiwon Lafiya Adewole

Babu karanci maganin cizon maciji a Najeriya – Ministar kula da kiwon Lafiya Adewole

- Ferfesa Adewole ya ce akwai maganin cizon maciji ajiye a maa'ikatar kiwon lafiya

- Adewole ya ce tun a shekara 2016 gwamnatin tarayya ta sayo magungunar cizon maciji daga kasar Amurka

- Ministar ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iy cigaba da daukan nauyin sayo ma jihohi maganin cizon maciji ba

Ministar kula da kiwon lafiya, Ferfesa Isaac Adewole, ya karyata jita-jitan da ake yadawa, na cewa maganin cizon maciji ya kare a Najeriya.

Ministar ya mayar da martani ne akan rahoton mutuwar mutane 250 sakamakon karancin maganin cizon maciji a jihar Gombe da Filato a cikin makonni 3.

A jawabin da Adewole yayi a zantawar da yayi da yan jarida a ranar Litinin, ya ce har yanzu akwai maganin cizon maciji ajiye a ma’aikatar kula da kiwon lafiya.

Babu karanci maganin cizon maciji a Najeriya – Ministar kula da kiwon Lafiya Adewole
Babu karanci maganin cizon maciji a Najeriya – Ministar kula da kiwon Lafiya Adewole

Tun a shekara 2016 gwamnatin tarayya ta sayo magungunar daga kasar Amurka, kuma duk jihar da ta nuna tana bukata, ana bata,” cewar ministar.

KU KARANTA : EFCC ta bayyana dalilin da ya sa wasu jihohi basa iya biya albashi

“Jihohin da suka samun wannan matsala, sun same ta ne, ta dalilin kin bin sabobin dokokin karban magani daga ma’aikatar kiwon lafiya, shiyasa suka kasa karban maganin cizon macijici daga ma’aikatar.

Ministar yayi kira da jihohi da su fara sayan magungunar cizon maciji a jihohin su, saboda gwamnatin tarayya ba za ta iya cigaba da dauka nauyin sayo mu su magungunar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: