Daga karshe! Gwamnatin Tarayya ta samar da maganin cizon maciji
- Daga karshe dai magungunan cizon maciji guda 5000 sun iso Najeriya daga kasashen Ingila da Costa Rica
- Tuni an raba magungunan zuwa asibitoci da dama da ke Jihohin Najeriya
- Ana sa ran isowar wasu magungunan guda 10,000 nan da kankanin lokaci domin kaucewa fadawa irin halin da aka shiga a watan da ya wuce
Bayan an shafe misalin wata daya ana karancin magungunan cizon maciji a wadda yayi sanidiyar mutuwar mutane da dama a jihohin kasar, Gwamnatin Tarayya ta sayo magungunan guda 5000.
Magungunan da aka siyo daga kasashen Ingila da Costa Rica sun iso Najeriya ne a karshen makon da ya gabata. Magungunan sun huda da EchiTAB G da kuma EchiTAB Plus wadda yake maganin cizon bakin kumurci da ma wasu macizan.
Magungunan da aka siyo a watan Augusta sun kare a cikin watan Satumba, hakan ya jifa majinyata cikin halin kakani-kayi musamman tunda anfi samun yawan cizon macijin a lokacin da ake girbe amfanin gona.
Wakilan kamfanonin da suka samar da magungunan cizon macijin a Najeriya, Dr. Nandul Durfa yace magungunan guda 3000 sun iso ne daga kasar Costa Rica sannan 2000 daga Ingila.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya kaddamar da gadar sama mai tsawon mita 700 da zata hada Najeriya da Kamaru
A cewar Durfa, karancin magunguna ya faru ne a dalilin rashin yin oda akan lokaci, yace nan da kwanaki kadan wasu magungunan guda 10,000 zasu iso kasar domin a kiyaye irin wannan karancin da ya faru.
Yace za'a raba magungunan ga asibitocin Jihohin Kaltungo, Gombe, Zamko na garin Langtang da ke Jihar Filato. Wasu kuma za'a aika dasu zuwa Makudi, Bunuwe, Taraba, Borno da kuma Adamawa.
Durfa yace nan gaba ana sa ran kera magungunan a Najeriya domin samun sauki. Ya kuma gargadi al'umma da suyi taka tsantsan da magunguna jabu da kuma wadanda ake kawowa daga kasar Indiya domin wannan anyi ta ne kawai domin magance cizon macizan da ke kasar Indiya, shi kuwa wanda aka siyo daga Ingila da Costa Rica anyi shi bayan an tafi da macizan Najeriya zuwa can kasashen sannan aka tatsa dafin su kafin akayi maganin.
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng