Birtaniya Ta Yi Magana bayan Kama Tsohon Sojanta da AK47 da Dama a Najeriya
- Kasar Birtaniya ta karyata rahoton cewa wani daga cikin jami’anta ne wanda hukumar DSS ta kama a filin jirgin saman Lagos
- Rahotanni sun ce an kama farin mutumin ne bisa zargin sayen makamai da harsasai don tayar da tarzoma a Warri, jihar Delta
- Birtaniya ta bayyana cewa mutumin da ake magana a kansa ya taba aiki ne a matsayin ma’aikacin wucin gadi, kuma an sallame shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Birtaniya a Najeriya ya karyata rahoton da ke cewa mutumin da jami’an DSS suka kama a filin jirgin saman Legas yana cikin jami’an sojinta.
Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun bayyana cewa mutumin na shirya wani yunkuri na kawo hargitsi a yankin Warri, jihar Delta.

Asali: Getty Images
A cewar rahoton Daily Trust, an kama wani mutum ne dan kabilar Itsekiri wanda ake zargin yana aiki da wata rundunar soji ta ketare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce mutumin ya sayo makamai da harsasai a madadin wani mai suna Collins don tayar da rikici a jihar Delta.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ofishin jakadancin Birtaniya ya ce mutumin ba jami’in sojin kasar ba ne a halin yanzu, kuma ba ya da wata alaka da su.
“Ya taba aiki da mu a baya” — Birtaniya
Sanarwar da Birtaniya ta fitar ta nuna cewa mutumin da aka kama ya taba alakar soji da ita na wani lokaci.
Ofishin jakadancin ya ce:
“Mutumin da ake magana a kansa ya taba zama sojin wucin gadi, amma yanzu ba ya cikin dakarun rundunar sojin mu.”
Haka kuma, Birtaniya ta ce ba ya cikin manyan jami’ai a lokacin da yake cikin rundunar, domin baya cikin cikakkun 'yan kasarta a wancan lokacin.
Ofishin jakadancin Birtaniya ya ce akwai dokar kare bayanan ma’aikata da ta hana su bayyana cikakkun bayanai game da tsofaffin ma’aikata ko masu aiki.
Don haka ta bukaci kafafen yada labarai su daina danganta mutumin da rundunar sojin Birtaniya domin kare gaskiya.
Yadda aka kama mutumin da makamai
A cewar rahotan Punch, DSS ta ce an kama mutumin ne a wani gari kusa da Asaba, inda aka cafke wasu mutane da ke tare da shi.
An ce an kwace bindigogi kirar AK-47 fiye da 50, da wasu bindigogi shida da harsasai sama da 3,000 daga hannunsu.
Bayan haka, rahoton ya ce DSS ta sake kama shi a Legas yayin da yake ƙoƙarin barin Najeriya zuwa Birtaniya. Sai dai ba a bayyana sunan mutumin ba domin dalilan tsaro da bincike.

Asali: Facebook
Birtaniya ta bukaci kafafen yada labarai su rika duba gaskiya kafin wallafa irin waɗannan labarai.
Ana sa ran hukumomin tsaro na Najeriya za su ci gaba da bincike kan makaman da aka kama da mutumin.
Rumbun makaman sojoji ya kone a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa rudunar sojin Najeriya ta sanar da samun hadari a rumbun makamanta a Maiduguri.
A daren ranar Alhamis, 30 ga Afrilu aka shiga firgici a birnin Maiguguri na jihar Borno saboda jin karar fashe fashe.
Sai dai daga baya rundunar sojin Najeriya ta ce tsananin zafi ne ya jawo fashewar makamai a barikin Giwa, ba hari aka kai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng