Babbar Matsalar da Matawalle Ya Tare wa APC a Zamfara ana Shirin Zaɓe

Babbar Matsalar da Matawalle Ya Tare wa APC a Zamfara ana Shirin Zaɓe

  • Bello Matawalle ya shiga tsakani bayan tsofaffin kansiloli 588 a Zamfara sun yi barazanar ficewa daga APC saboda rashin biyansu hakkokinsu
  • Tsohon gwamnan ya bukaci mambobin kungiyar su hakura, su ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC
  • Tsofaffin kansilolin sun amince su sake nazarin matakinsu tare da tallafa wa takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya shiga tsakani domin shawo kan tsofaffin kansiloli 588 a jihar Zamfara da suka yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki.

Matawalle ya roki mambobin kungiyar tsofaffin kansilolin da su yi watsi da shirin sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa, tare da ci gaba da kasancewa cikin APC.

Matawalle ya taka rawa wurin toshe matsala a APC
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Ministan ya yi wannan kira ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar tsofaffin kansiloli a gidansa da ke garin Maradun, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

An rasa rai bayan rikici ya ɓarke tsakanin makiyaya da tawagar kamfen siyasa

Muhimmancin tsofaffin kansilolin a siyasa

Kungiyar ta kunshi tsofaffin kansiloli 588 da suka taba wakiltar mazabu 147 a fadin jihar Zamfara.

Matawalle ya bayyana cewa tsofaffin kansilolin na da matukar tasiri a harkokin siyasa saboda kusancinsu da al'umma a matakin karkara.

Ya ce ya saurari korafe-korafen da suka gabatar masa, inda ya bukace su da su yi hakuri maimakon daukar matakin barin jam’iyyar.

Ministan ya kuma yi alkawarin tattaunawa da su tare da hada kai wajen shirya ayyukan siyasa domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Ya bukace su da su koma mazabunsu domin wayar da kan jama'a da tara goyon bayan APC da sauran 'yan takararta a dukkan matakan zabe.

Matawalle ya dakatar da tsofaffin kansiloli 588 barin APC
Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Facebook

Dalilin barazanar ficewarsu daga APC

Tun da farko, shugaban kungiyar, Bello Abdullahi, wanda ya taba wakiltar mazabar Gwaran da ke karamar hukumar Talata Mafara, ya ce sun kai wa ministan ziyara ne domin sanar da shi matsalolinsu.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Atiku Abubakar ya yi wa mutane da ADC ta je kamfen ADC a Bauchi

Ya bayyana cewa sun fara tunanin ficewa daga APC ne saboda gwamnatin jihar Zamfara ta kasa biyansu hakkokinsu da alawus-alawus din da suke bin ta.

A cewarsa, mambobin kungiyar sun hada da kansilolin da suka yi aiki tsakanin shekarar 2011 zuwa 2023 a mazabu 147 na jihar.

Abdullahi ya ce gwamnatin jihar ta yi watsi da su, lamarin da ya sa suka fara shirin komawa wata jam’iyyar siyasa, cewar Tribune.

Sai dai ya bayyana cewa shiga tsakanin Matawalle ya sa suka sake tunani, inda suka amince su ci gaba da zama a APC.

Shugaban kungiyar ya kuma tabbatar da cewa za su yi aiki domin ganin Tinubu ya sake lashe zabe, tare da tabbatar da nasarar dukkan 'yan takarar APC a Zamfara a babban zaben 2027.

Matawalle ya fadi babban burinsa a 2027

Mun kawo muku rahoton cewa Bello Matawalle ya bayyana cewa babban burinsa bayan gudanar da aikinsa a Ma’aikatar Tsaro shi ne taimakawa Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027.

Ministan ya buƙaci mambobin APC a Zamfara su haɗa kai tare da ƙara himma wajen yaɗa manufofin jam’iyyar da neman nasararta.

Matawalle ya yi alƙawarin tura ƙarin jami’an tsaro kan manyan hanyoyin Zamfara domin kare matafiya daga hare-haren ’yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.