Sani Hamza
5110 articles published since 01 Nuw 2023
5110 articles published since 01 Nuw 2023
Makiyaya dauke da miyagun makamai sun harbe Fr. Atongu a hanyar Makurdi–Naka, sun sace mutum 2. An garzaya da shi asibiti domin likitoci su ceto rayuwarsa.
Rashin kulawa, kayan gini marasa inganci, da rashin bin ka'idoji sune manyan dalilan rushewar gine-gine da ke ci gaba da jefa rayuka cikin haɗari a Najeriya.
Rikici tsakanin maharba da makiyaya ya jikkata Fulani tara a Bali, Taraba. Lamarin ya samo asali ne daga gardama kan shayar da dabbobi ruwa a rijiyar garin.
Tace fina-finai a Kano na kare tarbiyya da addini, amma masana da ’yan fim na ganin hakan na tauye fasaha da ’yancin fadin albarkacin baki da kuma dakile Kannywood.
Atiku Abubakar ya gana da Aregbesola a Osun, yayin da magoya bayansu ke rera wakar “Tinubu zai sha kasa a 2027”, inda ake zaton sun tattauna kan kawancen adawa.
Uwar gida, Zaliha Shuaibu ta amsa laifin kashe jaririn kishiyarta a Kaduna, ta ce Lawal Muhammad, ƙanin mijinta, ne ya ba ta gubar da ta kashe yaron da ita.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya ce rikicin cikin PDP ya hana shi kwanciyar hankali, don haka ya yanke shawarar barin jam'iyyar gabanin zaben 2027.
Duk da saukar farashi daga Dangote zuwa N875-N905, gidajen mai na sayar da man fetur a kan N890-N910, yayin da suke kukan asara saboda rage kudin da Dangote ke yi.
Majalisar wakilai ta bukaci Tinubu ya sanya dokar ta-baci a kan kiwon lafiya a Abuja. Ta nemi a inganta asibitoci da kuma daukar ma'aikatan lafiya a fadin birnin.
Sani Hamza
Samu kari