Muhammad Malumfashi
19805 articles published since 15 Yun 2016
19805 articles published since 15 Yun 2016
Bankin CBN bai san yadda zai yi da tashin da Dala ta ke yi ba. Hakan ya jawo masu gidajen mai su na son saidawa ‘Yan Najeriya litar man fetur a kan kusan N700.
Kwankwaso da ‘Yan Kwankwasiyya gamu da cikas a siyasa, rigima ta kusa cinye NNPP. Shugaban rikon kwarya ya ce za a hukunta Dr. Boniface Okechukwu Aniebonam.
Matakin taimakawa daliban Kano a BUK ya jawo Hadimin Buhari ya yabi NNPP. Wasu sun ce Gwamnatin Kano ta kyauta da za ta biyawa ɗaliban BUK kuɗin makaranta.
Duk tulin kuri'un da LP ta samu a Ojo a zaben 'dan majalisa sun tashi a banza. Kotun sauraron karar zaben Legas tayi hukuncin da bai yi wa 'yan adawa dadi ba.
An ji magoya baya sun shiga duhu a sakamakon haduwar Rabiu Musa Kwankwaso da Bola Tinubu bayan zaman da jigon na NNPP ya yi da Atiku Abubakar a gidansa kwanaki.
Rahoton nan ya nuna yadda matasa masu ruwa da tsaki a APC su ka samu sabani a junansu a game da wanda ya dace ya zama ministan harkokin matasa a gwamnati mai-ci
David Umahi ya duba ayyuka a titunan Abuja zuwa Lokoja kuma ya yi bakin cikin abin da ya gani. Ministan bai gamsu da aikin da ake yi a titin na Abuja-Lokoja ba.
PHALGA sun hada-kai da ‘yan sanda wajen kama wasu da ake zargin ‘yan damfara ne. An cafke ‘Yan Yahoo-Yahoo din ne bayan an zarge su da birne wani yaro da rai.
Injiniya Abubakar Momoh ya zama Sabon ministan Neja-Delta a Najeriya. Momoh ya bayyana Sanata Adams Oshiomhole a matsayin wanda ya kai sunansa zuwa Aso Rock.
Muhammad Malumfashi
Samu kari