Tsohon Hadimin Buhari Ya Yabawa Kokarin Gwamna Abba Gida Gida a Jihar Kano

Tsohon Hadimin Buhari Ya Yabawa Kokarin Gwamna Abba Gida Gida a Jihar Kano

  • Ganin yadda dalibai su ka gaza biyan kudin karatu, gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta tallafawa Kanawa
  • Bashir Ahmaad wanda cikakken ‘dan APC ne, ya fito baro-baro ya na mai jinjinawa gwamnati mai-ci
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na mulki a jihar Kano ne a karkashin NNPP bayan kifar da APC a zaben 2023

Abuja - Hausawa su na cewa yabon gwani ya zama dole, abin da ya faru da gwamnatin Abba Kabir Yusuf kenan da ke mulkin Kano.

Bashir Ahmaad wanda ya yi aiki da Muhammadu Buhari na fiye da shekaru bakwai tsakanin 2015 da 2023, ya yabawa gwamnatin NNPP mai-ci.

Gwamnan jihar Kano ya sanar da cewa ya ware makudan miliyoyi domin biyan kudin karatun ‘yan jihar Kano da ke jami’ar nan ta Bayero.

Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abba Gida Gida ya ceci 'Yan Kano

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Kwanakin baya aka kara kudin makaranta a jami’ar, hakan ya jefa yaran talakawa a ha’ula’i, har ta kai 'yan majalisa sun fara taimaka masu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da cikakken ‘dan jam’iyyar APC ne shi a jihar Kano, 'dan takaran majalisar ya na ganin Mai girma Abba Yusuf ya cancanci a jinjina masa.

Yayin da gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida ya bada sanarwar haka a dandalin Facebook, Bashir ya ce: “A nan gwamnati ta kyauta.”

Bayan haka, hadimin tsohon shugaban kasar ya fitar da gajeren bayani a shafinsa, ya ajiye sabanin siyasa, yake cewa gwamnati tayi kokari.

"Na jinjinawa gwamna Abba Kabir Yusuf a kan yunkurinsa na cigaba ta hanyar amincewa da adadin Naira miliyan 700 domin biyan kudin karatun dalibai 7000 a jami’ar Bayero ta (BUK)."

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Magana Kan Sabon Rikicin Da Ya Ɓarke a Jam'iyyar APC, Ya Gana da Gwamnan Arewa

- Bashir Ahmad

Ihu bayan hari aka yi a Kano?

Yayin da wasu su ka yi ikirarin dalibai da-dama sun ga biyan kudin a lokacin da sanarwar ta fito, sai ya ce kyau a maida masu kudinsu.

Masu maida martani su na ta yi, har da masu cewa matashin bai taya Abdullahi Ganduje murnar zama shugaban jam’iyyar APC na kasa ba.

Mukhtar Mudi Sipikin ya nemi takarar ‘dan majalisa a jam’iyyar PRP, shi ma ya yaba da tsarin yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a jiya.

"Haƙiƙa Gwamnatin Kano ta kyauta da za ta biyawa ɗaliban BUK kuɗin makaranta."

- Mukhtar Mudi Sipikin

Kano: An kori karar Abba Kabir Yusuf

A karshen zaman da aka yi a kotun Abuja, ana da labari Alkalai sun yi kaca-kaca da Lauyan Gwamnan Kano, Adegboyega Awomolo.

Adegboyega Awomolo (SAN) ya kalubalanci shaidar da aka kafa da Dr. Aminu Idiris Harbau a kotun sauraron karar zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel