Alkalai Sun Yi Fatali da Rokon Abba Gida Gida a Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kano

Alkalai Sun Yi Fatali da Rokon Abba Gida Gida a Shari’ar Zaben Gwamnan Jihar Kano

  • Abba Kabir Yusuf ya je kotun daukaka kara da nufin a ki karbar hukuncin shari’ar zaben Gwamnan 2023
  • Mai girma Gwamnan ya na kalubalantar yadda kotun karar zabe ta karbi shaidar Aminu Idiris Harbau
  • Ana fafatawa a kotu tsakanin APC, Nasir Yusuf Gawuna a kan nasarar jam’iyyar NNPP a zaben Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Kotun daukaka kara da ke zama a birnin Abuja, ya yi watsi da wata kara da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shigar a gaban ta.

Mai girma Gwamnan ya na so a jinginar da hukuncin kotun sauraron karar zaben gwamna na 2023, Tribune ta fitar da rahoton a ranar Alhamis.

Alkalan da su ka saurari karar su ne Obande Ogbuiya, Williams Daudu da Ridwan Abdullahi.

Gwamnan Jihar Kano
Jami'an Gwamnatin Jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Alkalai sun soki Gwamnan Kano

Mai shari’a Obande Ogbuiya da sauran abokan aikinsa sun ce akwai shiririta da ban-haushi a karar da lauyoyin gwamnan su ka shigar a gabansu.

Kara karanta wannan

Aiki ya fara: Daga zuwa, Ganduje ya yi sabbin nade-nade a kwamitin NWC na APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyoyin Abba Kabir Yusuf sun yi karar hukumar zabe na INEC da jam’iyyar APC a kan damar da aka ba Dr. Aminu Idiris Harbau na bayyana a kotu.

Aminu Idiris Harbau ya na cikin shaidun da jam’iyyar APC ta kira a shari’ar zaben gwamnan Kano, ya bada hujjojin da za su iya rusa nasarar NNPP.

Sauraron shaidar Dr. Aminu Idiris Harbau

Lauyoyin gwamnan sun ce kotu tayi kuskure da ta bari Harbau ya bayyana a cikin shaidun shari’ar. Labarin nan ya fito a jaridar Daily Trust a jiya.

Babban wanda ya tsayawa Mai girma gwamna Yusuf a kotun daukaka karar, Adegboyega Awomolo (SAN) ya na zargin an sabawa dokar zabe.

Awomolo (SAN) ya ce sauraron mai bada shaidar ya jawo an yi masa rashin adalci.

Haka zalika Mai girma gwamnan ya yi ikirari Mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya yi kuskure da ya saurari korafin APC alhali bai da hurumi.

Kara karanta wannan

Nasara a Kotun Zabe: Kwankwaso, Abba Gida Gida Da Wasu Jiga-Jigan NNPP Sunyi Taron Addu’a Na Musamman a Kano

Kotun daukaka karan da ke zama a garin Abuja ba ta gamsu da wannan da sauran hujjoji shida na lauyan ba, aka ki karbar bukatar da ya gabatar.

Kwankwaso tare da Bola Tinubu

A daren yau ne aka ji labari magoya baya sun shiga duhu a sakamakon haduwar Rabiu Musa Kwankwaso da shugaban Najeriya watau Bola Tinubu.

A watan Yuni, madugun Kwankwasiyyan ya je fadar Shugaban kasa, sun yi wata tattaunawa, sai kuma aka ga babu sunan shi cikin jerin ministoci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel