Yadda Sanatan APC Ya Zama Silar Samun Mukami na Wajen Tinubu - Sabon Minista

Yadda Sanatan APC Ya Zama Silar Samun Mukami na Wajen Tinubu - Sabon Minista

  • Abubakar Momoh ya ce bai yi tunanin shi ne zai zama Ministan harkokin Neja Delta a Najeriya ba
  • Ministan ya bayyana Sanata Adams Oshiomhole a matsayin wanda ya kai sunan shi zuwa Aso Rock
  • Injiniya Momoh ya yabi shugaba Bola Tinubu wanda yake cewa ya ba mutanen kowane yanki dama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Sabon ministan harkokin Neja-Delta, Abubakar Momoh ya ce bai taba tunanin shi zai zama wanda zai wakilci jihar Edo a majalisar FEC ba.

Abubakar Momoh ya yi wannan bayani a wajen bikin da aka shirya domin taya shi murnar samun wannan matsayi a Abuja, The Guardian ta kawo rahoton.

Bayan zaben shi a matsayin minista, kafin su shiga ofis tukuna sai Bola Tinubu ya canzawa Momoh ma’aikata daga ta matasa zuwa ta harkokin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Ana Rigima a Kan Kujerar Minista 1 Da Ta Ragewa Bola Tinubu Ya Nada a Gwamnati

Ministoci
Bola Tinubu ya rantsar da Ministoci Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Momoh ya yabawa salon Tinubu

A cewar Momoh, canjin wurin aikin da aka yi masa ya nuna Mai girma Bola Tinubu shugaba ne wanda yake sauraron al’umma, ya kuma yi abin yabo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ministan yake cewa a tarihin kasar nan, ba a taba samun mutumin Edo da ya rike ma’aikatar harkokin Neja-Delta ba, sai da Tinubu ya karbi mulki.

Injiniyan ya na ganin sabon shugaban Najeriyan ya yi abin da ya gagari har shugabannin mulkin soja, don haka ya cancanci a rika gode masa.

Tinubu ya tafi da kowa a mulkinsa

"A wuri na, daya daga cikin tarihin da ya kafa shi ne, ya tafi da mutanen kowane yanki a Najeriya, ba tare da la’akari da wurin haihuwa ko kabila ba

Za ka iya zama Ministan birnin tarayya; yayin da mutane su ke tunanin ba zai taba yiwuwa ba.

Kara karanta wannan

Wike: Sabon Minista Ya Yi Alkawarin Cusawa Ma’aikatansa Cutar Hawan Jini

Mu na godewa Ubangiji da ya ba mu Shugaban kasan da ya ke bude kofa ga duk mai neman ganin shi ko yake da wani bayanin da zai kawo masa.

Mu na godewa Ubangiji da ya ba mu Shugaban kasan da ya ke da kunnuwan sauraron duk wanda ya ke da wani abin da zai fada masa.

Adams Oshiomhole ya kawo minista

Rahoton ya ce Momoh ya ji dadin yadda Sanata zai iya bada sunan wanda zai zama ministan tarayya, a dalilin haka ya godewa Adams Oshiomhole.

Shi kuwa Sanata Adams Oshiomhole ya yabi ministan da cewa sun dade tare a siyasa, ya na fatan shi da abokan aikinsa za su yi abin da za a yaba.

Wa zai zama ministan matasa?

Shugabannin matasa 32 aka ji labari sun ce ba su goyon bayan Dayo Israel ya zama Ministan harkokinsu a Najeriya, sun ce a bar komai ga Seyi Tinubu.

Kara karanta wannan

FCT: Shehu Sani Ya Fadi Rigimar Da Wike Zai Janyowa Kansa Da Tinubu Idan Ya Ƙi Bi a Hankali

Hadimin shugaban kasa, Olusegun Dada da ya taba neman kujerar, ya ce ba hurumin matasa ba ne, ya na ganin a kyalewa Bola Tinubu wuka da nama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel