Ana Wahala Fa: Malami Ya Roki Gwamna Ya Kawowa Talaka Agaji Bayan Tallata APC

Ana Wahala Fa: Malami Ya Roki Gwamna Ya Kawowa Talaka Agaji Bayan Tallata APC

  • Shuaibu Salihu Zariya ya ankarar da masu mulki a kan kuncin rayuwar da al’umma su ka shiga
  • Malamin ya roki gwamnatin jihar Kaduna ta fito da tsare-tsaren rage radadin talauci da matsi
  • Shehin ya bada shawarar a raba tallafin da shugaban kasa ya bada, a tabbata jama’a sun ci moriya

Kaduna - Shuaibu Salihu Zaria malamin addinin musulunci ne a garin Zariya, jihar Kaduna, ya aika sako na musamman zuwa ga Malam Uba Sani.

A wani fai-fai da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a dandalin Facebook, an ji Sheikh Shuaibu Salihu Zaria ya na mai jan hankalin gwamnatin APC.

Bayan jinjina da yabo musamman ganin yadda aka rage kudin karatu a manyan makarantun gwamnati Kaduna, malamin ya na rokon arziki.

Kara karanta wannan

Ana tsaka mai wuya: Abin da Tinubu ya fadawa Malaman addini kafin su tafi Nijar

Malami
Sheikh Shuaibu Salihu Zariya da Gwamna Uba Sani Hoto: Shuaibu Salihu Zaria/Uba Sani
Asali: Facebook

A duba lamarin talaka

Wannan malami ya yi wa mai girma gwamna Uba Sani fatan alheri, sannan ya nemi alfarmar a fito da tsare-tsaren da za su ragewa talakawa radadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mu da mu ka ce a zabe ku, a kullum mu na cikin talakawa, mu na ganin irin kokensu. Su na kwana ba su ci ba, rana ta yi ba su ci ba, dare ya yi ba su ci ba.
Kuma babu kudi a aljihunsu, don Allah Mai girma gwamna yadda ka bi sako-lungu ka tabbatar da samu kuri’ar talaka, ka tabbatar ka sanyayawa talaka."

- Sheikh Shuaibu Salihu Zaria

Masanin Al-Kur’ani da Hadisin ya kara da cewa su na da masaniyar N5bn da shugaban kasa ya warewa kowace jihar kasar nan domin marasa kafi.

"Yau mata su na zinace-zinace, ‘yan mata sun zama zaurawa, wasu sun zama karuwai. Wasu matan aure su ke wulakanta kan su domin su samu abinci.

Kara karanta wannan

Tallafin Biliyan 5: Tinubu Ya Fadi Abin Da Zai Yi Don Tabbatar Da Adalci A Rabon, Ya Roki Gwamnoni

Magidanta su na gudu su na barin gidajensu saboda talauci, don Allah shugabanni ku tausayawa talaka."

Tsoron a daina jin maganar malamai

Mu almajirai da malamanmu wadanda aka yi amfani da mu da wasunmu ana neman kuri’a, ba mu da abin da za mu cewa talakawan da mu ke karantarwa.

- Sheikh Shuaibu Salihu Zaria

Shehin ya ja hankalin gwamna Sani da cewa idan aka tafi a haka, za a je lokacin da almajirai za su daina sauraronsu idan sun fadi wanda za a zaba.

Kira zuwa ga talakawan Kaduna

Duk da wahalar da ake ciki a ko ina, Sheikh Zariya ya ce sun san fadi-tashin da masu mulki su ke yi, ya roki Uba Sani ya kyautatawa marasa hali a jihar.

A karshe malamin da ya yi karatu a kasar Saudi Arabiya ya ba talakawa shawarar su dage da yin addu’o’i, ya na cewa tsinewa jagororinsu ba mafita ba ce.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

A kara hakuri wajen gyaran Najeriya

A baya an ji Bola Tinubu ya na cewa shawo kan matsalolin Najeriya sai an yi hakuri, ba sha yanzu magani yanzu ba ne kamar yadda wasu su ke tunani.

Da yake magana ta bakin Sakataren gwamnati, George Akume, shugaban Najeriya ya ce wahalar da ake sha tamkar nakuda ne a wajen haihuwar jariri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel