‘Yan Adawa Sun Sake Rasa Kujerar Majalisa, Kotu Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zabe

‘Yan Adawa Sun Sake Rasa Kujerar Majalisa, Kotu Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zabe

  • Lanre Ogunyemi ya yi nasara a kotun sauraron karar zabe, an soke sakamakon zaben da ya shiga
  • Alkalan kotun karar zabe sun tabbatar da Seyi Sowunmi bai cancanci ya nemi takarar majalisa ba
  • Kotu ta kori ‘dan majalisar na jam’iyyar LP, ta ce ‘dan takaran APC mai-ci ne asalin mai kujerar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Kotun sauraron korafin zabe mai zama a Legas, t soke nasarar da Seyi Sowunmi ya samu a mazabar Ojo a takarar da aka yi.

The Nation ta ce an yanke hukunci cewa Honarabul Lanre Ogunyemi wanda ya yi takara a jam’iyyar APC ne ainihin wanda ya yi nasara.

Kotun karar zaben ta ba tsohon sakataren jam’iyyar APC na reshen jihar Legas nasara kan LP wanda ta fi kowa samun kuri’u a mazabar.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Alkalai Sun Yi Fatali da Rokon Abba Gida Gida a Shari’ar Zaben Gwamna

Majalisar Wakilan Tarayya
Shugabanni a Majalisar Wakilai Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

LP ta tsaida wanda bai cancanta ba

Tun da aka sanar da sakamakon zaben, Ogunyemi ya tafi kotu domin ya kalubalanci nasarar da hukumar INEC ta ba ‘dan takaran hamayya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoto ya ce alkalai uku da su ka saurari karar duk sun yi hukunci tun farko bai dace Seyi Sowunmi ya shiga takarar ba, bai cancanta ba.

Kujerun APC sun karu a majalisa

A sakamakon ruguza takarar ‘dan adawar ta fuskar doka, alkalan sun ba jam’iyyar APC kujerar, ‘dan takaranta ne zai tafi majalisar wakilai.

Wannan sabon hukunci ya na nufin kujerun APC mai rinjaye za su kara yawa idan aka tafi a haka bayan nasarori a Delta da kuma Kano.

A dokar kasa da tsarin mulki, ‘dan majalisar ya na da damar da zai daukaka kara idan bai gamsu zuwa babban kotun daukaka kara na kasa.

Kara karanta wannan

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Shugaban Fitacciyar Jam'iyya Na Ƙasa, Ta Bayyana Sunan Sabon Shugaba

Kamar yadda labari ya fito daga Daily Trust, Ashu A. Ewah ya jagoranci shari’ar tare da abokan aikinsa, Abdullahi A Ozegya da M A Sambo.

A ‘yan makonnin nan, APC mai mulki a Najeriya ta samu nasarori akalla uku a kotun da su ke sauraron korafi a game da zabukan shekarar nan.

LP ta na asarar kuri'u da 'yan majalisa

LP mai kujeru 38 a majalisar tarayya ta na cigaba da rasa ‘ya ‘yanta inda a baya aka tsige Ngozi Okolie mai wakiltar Aniocha/Oshimili a Delta.

Mai shari’a A.Z. Mussa ya ce an yi kuskure, Ndudi Elumelu na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben, hukuncin da bai yi wa 'yan adawa dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel