Yadda Ake Sauraron Shari’ar Zaben Abba Gida Gida v Nasiru Gawuna a Kotu (Kai-Tsaye)

Yadda Ake Sauraron Shari’ar Zaben Abba Gida Gida v Nasiru Gawuna a Kotu (Kai-Tsaye)

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A safiyar Juma’a, kotun daukaka kara mai zama a birnin tarayya watau Abuja za ta yanke hukunci a shari’ar zaben Gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602 a zaben da aka yi, Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya zo na biyu ya samu kuri’a 890,705.

Da APC ta je kotun daukaka kara, Alkalai sun rage fiye da 165, 000 daga cikin kuri’un NNPP saboda rashin sa hannu da hatimi, aka ba APC nasara.

Shari’ar nan ne Abba Kabir Yusuf ya kalubalanta a wannan kotu, APC kuma ta roki a tabbatar da hukuncin da karamar kotun zaben ta zartar a Satumba.

Kotu ta tsige Abba Kabir Yusuf

Bayan sauraron shari'ar, Alkalan kotun daukaka kara sun tsige Abba Kabir Yusuf bisa dalilali da hujjojin jam'iyyar APC.

Abba Gida Gida 'Dan NNPP ne ko a'a?

Kotun daukaka kara ta sake ba Kotun korafin zabe gaskiya da ta ce Abba Kabir Yusuf ba cikakken ‘dan jam’iyyar NNPP ba ne.

Premium Times ta rahoto cewa kotun daukaka kara ta ce ya kamata a rusa takarar Abba a jam'iyyar NNPP tun a karamar kotu.

Hukuncin Kano ta Zoom

Kotun ta zartar da cewa yin hukunci ta Zoom a maimakon a zauna a harabar kotu ba laifi ba ne, an yi watsi da korafin Wole Olanipekun

Nasiru Gawuna ya kubuta?

Barista Hikima wanda yake kawo bayanai daga kotun ya rubuta a shafinsa cewa kotu ta ce:

"Ba dole bane sai APC ta saka sunan Nasir Gawuna wajen shigar da kara ba." -

P1730: Kotun karar zabe ta yi daidai

Kotun daukaka kara ta ce karamar kotu ba ta saba doka da ta karbi takardun da lauyoyin jam'iyyar NNPP su ke adawa da su ba.

Kotu ta fara karanto hukunci

Majiya daga kotun daukaka karan ta ce Alkalai sun fara karanto hukunci, an soma yin shimfidar korafin lauyoyin Gwamnan Kano.

An fara shirin karanto kara

Kamar yadda Barista Hikima ya fada a shafinsa, hukunci hudu za a yanke a zaman yau; uku daga NNPP sai kuma guda daga APC.

Jami'an tsaro a kotu

Abba Hikima wanda shahararren matashin lauya ne a Kano, ya fada a Facebook cewa an baza jami'an tsaro kafin a fara shari'ar.

A Kano ma an dauki matakai masu tsauri domin gudun rikicin siyasa ya barke.

Shari'ar Kano
Motocin jami'an tsaro wajen shari'ar zaben Kano Hoto: Abba Hikima
Asali: Facebook

Kotu ta zauna

Ibrahim Arif Garba wani lauya ne wanda yana kotun domin jin shari'ar zaben Gwamnan na Kano, ya shaida cewa an fara zama.

Kamar yadda sanarwa ta zo, zuwa karfe 10:00 ko kimanin haka za a fara hukunci.

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng