Wasu Sun Tsinke Da Lamarin Tinubu da Kotu Ta Tsige Gwamnonin Adawa 3 a Kwana 4

Wasu Sun Tsinke Da Lamarin Tinubu da Kotu Ta Tsige Gwamnonin Adawa 3 a Kwana 4

  • Jama’a da-dama sun soki hukuncin da kotun daukaka kara ta zartar na tsige Gwamna Caleb Mutfwang a jihar Filato
  • Daga Alhamis zuwa Lahadi, Alkalai sun tunbuke Gwamna Abba Kabir Yusuf da Gwamna Lawal Dare na jam’iyyun adawa
  • Mafi yawan hukuncin da ake yi sun taba jam’iyyun hamayya ne illa a jihar Nasarawa da kotu ta tsige gwamnatin APC

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jama’a sun fara yin Allah wadai da yadda kotu ta ke raba gwamnonin jihohin adawa da kujerunsu, ana ba APC mai mulki nasara.

A cikin kwanaki hudu, jam’iyyun PDP da NNPP sun rasa iko da jihohin Zamfara, Kano da Filato, hakan ya jawo mutane sun fara tsorata.

Wasu suna ganin an kama hanyar maida Najeriya tsarin jam’iyya daya kamar yadda Atiku Abubakar ya fara kira da babban murya a baya.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fayyace ainihin sababin tsige Abba, gwamnan Filato a Kotu

Zaben APC
Yakin zaben APC a Bayelsa Hoto: @OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane na sukar Kotu da APC

Masu tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta sun yi tir da hukuncin da Alkalan kotu su ka yi, ana ta zargin APC da bankara shari’a.

Wani Najeeb Datti yake cewa idan haka za a rika tafiya, babu dalilin INEC ta kashe kudi a gudanar da zabe, sai a bar APC a kan mulki kurum.

Ja’afar Ja’afar wanda ‘dan jarida ne ya koka bayan ganin hukuncin zaben gwamnan Filato.

"Matukar kuri’un rinjayen mutane ya daina tasiri, kotu ta daina bin doka, majalisa ta zama ‘yar amshin shatan shugaban kasa, to ba damukaradiyya ake yi ba.”

Can kuma ya ce:

"Duk wanda ke murna saboda zalunci ya yi masa rana, to wata rana sai ya yi kukan neman adalci ya rasa."

- Ja’afar Ja’afar

Jam'iyyar APC ta karyata zargin jama'a

Kara karanta wannan

Jama'a sun hada-kai, sun yi karar Bola Tinubu a kotu kan nade-naden shugabannin INEC

Punch ta ce Darektan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim ya ce zargin da ake yi masu na na murkushe adawa sam ba gaskiya ba ne.

A cewar Bala Ibrahim, masu wannan magana ba su san yadda kotu ta ke yin aiki ba ne.

Wani mai bibiyar siyasa, Aly Bunza ya yi masu raddi da cewa haka kotu ta karbe masu kujeru a zaben 2019, amma ba a zargi kowa da zalunci ba.

Wadannan koke suna zuwa ne kwanaki kadan bayan jam’iyyar APC ta samu gagaruman nasara a zaben gwamnonin jihohin Kogi da Imo.

Akwai masu ganin APC ta yi murdiya a zabukan nan duk da PDP ta zarce a jihar Bayelsa.

Nyesom Wike ko Atiku a PDP?

An rahoto Dr. Umar Ardo ya na cewa mafi rinjayen shugabannin jam’iyyar PDP ba su tare da Atiku Abubakar har yanzu duk da shi ya yi takara.

Atiku ya dawo PDP ne a 2017 bayan ya tafi APC neman mulki, Ardo yake cewa a lokacin Wike ya na Gwamna ya samu damar juya jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel