Danyen Zanga Zanga Ya Biyo Bayan Tunbuke Gwamnan PDP da Kotu Tayi a Jihar Filato

Danyen Zanga Zanga Ya Biyo Bayan Tunbuke Gwamnan PDP da Kotu Tayi a Jihar Filato

  • Hukuncin kotun daukaka kara bai yi wa wasu dadi a jihar Filato ba, musamman magoya bayan jam’iyyar PDP
  • Tun jiya aka samu labari mutane sun fara fita zanga-zanga a garuruwan Filato saboda an tsige Gwamnan jihar
  • Zuwa yanzu Mai girma Caleb Mutfwang bai yi magana ba, ana sa rai cewa jami’an tsaro za su kare rai da dukiyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Plateau - Zanga-zanga sun barke a garin Jos inda nan ne babban birnin jihar Filato a sakamakon hukuncin kotun daukaka kara.

Caleb Mutfwang
Kotu ta tsige Gwamnan Jihar Filato Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Twitter

Leadership ta ce sauke Gwamna Caleb Mutfwang da aka yi ya jawo rashin jin dadi a Filato, wasu ba su ji dadin hukuncin kotu ba.

Kotu ta tsige Gwamnan Filato

A yammacin ranar Lahadi, kotun daukaka kara da ke zama a garin Abuja ta tsige Mai girma Barista Caleb Mutfwang daga kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Tsohon Sanatan APC Ya Yi Allah Wadai da Kotu a Kan Tsige Gwamnonin PDP da NNPP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kadan bayan samun labarin hukuncin, rahoton ya ce sai aka fara guna-guni a jihar, hukuncin kotun ya jawo firgici a jihar ta Filato.

Wuraren da ake zanga-zanga a Filato

A karamar hukumar Jos ta Kudu, matasa masu goyon bayan jam’iyyar PDP sun yi dandazo a shatale-talen Gyel domin yin zanga-zanga.

Magoya bayan na jam’iyyar PDP ba su gamsu da hukuncin da alkalan su ka zartar a kan zaben Gwamnan Filato da aka yi a farkon bana ba.

Haka abin yake a yankin Anguwan Rukuba da ke karamar hukumar Jos ta Arewa tun jiya.

Duk da gargadin 'yan sanda, ‘yan jam’iyyar PDP da sauran mazauna garin Riyom sun fita zanga-zanga domin su nunawa duniya fusatarsu.

Meyasa mutanen Filato su ke zanga-zanga?

Wani jagoran matasa a garin Mangu, Hon. Pankyes Yamsat ya shaidawa manema labarai sun zabi yin zanga-zanga kan tsige Mutfwang.

Kara karanta wannan

Wasu sun tsinke da lamarin Tinubu da Kotu ta tsige gwamnonin adawa 3 a kwana 4

Pankyes Yamsat ya na ganin cewa Mutfwang shi ne zabin al’umma, amma an yi amfani da kotu domin maidawa APC mulki a Filato.

Wani mazauni kuma ma'aikaci a yankin 'Yan wase a jihar ta Filato, ya shaidawa Legit cewa akwai yiwuwar a cigaba da zanga-zanga.

Malam Ibrahim Abdulrahman ya ce tun da aka ji hukuncin da kotu ta yi wasu su ka fara zanga-zanga cikin dare, kuma lamarin bai lafa ba.

APC za ta karbe kujerun adawa?

Ana da labari cewa mutane sun fara surutu da Kotu ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda shi kadai ya samu kuri’u fiye da miliyan a 2023.

Kafin nan kotun daukaka kara ta ce za a sake maimaita zaben Gwamna a wasu garuruwa a Zamfara bayan zargin magudi a zaben Kogi da Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng