Takaitaccen Tarihin Ahmed Usman Ododo da Ya Lashe Zabe Zai Gaji Yahaya Bello a Kogi

Takaitaccen Tarihin Ahmed Usman Ododo da Ya Lashe Zabe Zai Gaji Yahaya Bello a Kogi

  • Ahmed Usman Ododo ya rike babban mai binciken kudin kananan hukumomin jihar Kogi zai zama sabon Gwamna a APC
  • Zababben Gwamnan Kogi ya kware a fannin akanta da kula da kudi, ya na da rajista da kungiyoyin ICAN, ANAN da kuma IIA
  • Duk da babu wasu bayanai sosai a game da Gwamnan mai jiran gado, ya na da digirin farko da na biyu daga ABU da UNILAG

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kogi - Mun kawo gajeren tarihin Ahmed Usman Ododo ganin hukumar INEC ta sanar da cewa shi ya zo na farko a zaben gwamnan jihar Kogi.

A cikin 'yan takaran da aka gwabza da su a zaben 11 ga Nuwamba, shi ya yi dace, karo na biyu da Ebira zai zama gwamna cikin shekaru 32.

Kara karanta wannan

Kwace kujerar Abba na jihar Kano alama ce ta Tinubu zai samu tazarce a 2027, Jigon PDP, Omokri

Ahmed Usman Ododo
Ahmed Usman Ododo a fadar shugaban kasa Hoto: @OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Wanene Ahmed Usman Ododo?

1. Akwai sabani tun daga batun ranar haihuwar Ahmed Ododo, wasu sun ce an haife shi ne a 1960s, bayanin shafin Wikepedia ya nuna a 1982 aka haife shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Shakka babu, an haifi zababben Gwamnan ne a karamar hukumar Okene a jihar Kogi, saboda shi kabilar Ebira ne.

3. Ododo ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello a Zariya daga kuma digirgir jami’ar UNILAG da ke garin Legas.

4. BBC ta ce Gwamnan mai jiran gado ya yi digirinsa ne a bangaren akanta har ya na da shaidar CPA, ICAN da ANAN

5. Sai da Ododo ya shafe shekaru sama da bakwai a matsayin mai binciken kudin kananan hukumomin jihar Kogi.

6. Usman-Ododo ya taba shiga kungiyar majalisar matasa har ya jagorance ta Kogi kuma ya taba zama mai ba Gwamna shawara.

Kara karanta wannan

INEC ta mika satifiket ga sabon gwamnan APC, ya tura muhimmin sako

7. Daga baya ne ya zama shugaban hukumar da ke tattara haraji a Kogi a karkashin mulkin Yahaya Bello

8. Bello Matawalle ya gudanar da zaben fitar da gwanin da Ododo ya yi nasara a kan sauran ‘yan APC da kuri’u 78, 704.

9. ‘Dan takaran ya doke Smart Adeyemi da Mohammed Ozigi Salami yayin da su Edward Onoja su ka hakura da takarar.

10. Mai girma Yahaya Bello ya goyi bayan Ododo har ya samu tikiti, kuma ya ba shi gudumuwa mai karfi a babban zabe.

Ya aka yi Ododo ya ci zabe a Kogi?

Dazu kun ji labari mun tattaro wasu abubuwa da ake ganin sun bada gudumuwa wajen nasarar APC da Ahmed Ododo a zaben jihar Kogi.

Sakamakon zaben INEC ya nuna ‘Yan kabilar Ebira sun dumbuzawa Ahmed Usman Ododo kuri’u a karshe sai dai Jam’iyyar SDP ta zo ta biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel