NNPP: Yadda Ganduje da APC Suka Shirya Tada Rigima Saboda Shari’ar Zaben Kano
- APC da NNPP sun shirya domin a safiyar yau Juma’a ne kotun daukaka kara za ta yi hukunci a kan zaben Gwamnan Kano
- Jam’iyyar NNPP ta kasa ta ce ta gano shugabannin APC na kasa da kuma na matakin jiha sun shirya tada rikici a Kano
- Hon. Abba Kawu Ali ya zargi takwaransa watau Abdullahi Umar Ganduje da Abdullahi Abbas da dauko hayar ‘yan daba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Jam’iyyar hamayya a Najeriya ta NNPP ta fitar da sanarwa inda ta zargi APC da shirin jawo rikici a jihar Kano a kan shari’ar zabe.
A wata sanarwa da aka samu daga shugaban NNPP na kasa, Hon. Abba Kawu Ali, jam’iyyar ta ce jagororin APC sun kitsa tashin-tashina.
Wani daga cikin hadiman Gwamnan jihar Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya wallafa sanarwar a shafinsa na Facebook a safiyar Juma’ar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP ta zargi Ganduje da shirin tada rikici a Kano
Hon. Abba Kawu Ali ya ce shugaban APC na kasa kuma tsohon Gwamna a Kano, Abdullahi Umar Ganduje da mutanensa ne da danyen aikin.
“Mun samu bayani mai karfi cewa shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, sun umarci a kawo ‘yan daba da za a ajiye a wasu muhimman wurare da nufin kawo tarzoma idan hukuncin kotun daukaka kara bai yi masu dadi ba.”
- Hon. Abba Kawu Ali
Shugaban NNPP na rikon kwaryan ya na cewa irin haka APC ta yi a zaben 2023, aka kona mutane a sakatariyar jam’iyyarta a garin Tudun Wada.
Shari'ar Kano: NNPP ta yi kira ga jami'an tsaro
Kano Focus ta rahoto Abba Ali ya na kira ga jami’an tsaro su dakile wannan shiri da ake yi duk da ana kokari wajen kare rayuka da dukiya a Kano.
"Abin takaici ne a ce shugaban APC na kasa da shugaban reshen jiha sun shirya tada rigima a wurin da ya dace su yi bakin kokarin tsare."
- Hon. Abba Kawu Ali
Jawabin ya kara da kira ga magoya bayan NNPP su zama masu bin doka, sannan mutanen Kano su sanar da hukuma idan sun ga wata barna.
Kwankwaso ya dawo gida
Ana tsakiyar shirin shiga kotun sai aka ji labari Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo Najeriya daga birnin Cairo a kasar Masar da ya tafi kwanaki.
Duk a yau ne kuma Abba Kabir Yusuf zai tura dalibai fiye da 100 da su yi digirgir a kasar waje kamar yadda kwamishinan ilmin Kano ya sanar.
Asali: Legit.ng