Ahmad Yusuf
11628 articles published since 01 Mar 2021
11628 articles published since 01 Mar 2021
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu za ta kaddamar da zanen da ya fu kowanne zane girma a duniya ranar Dimokuradiyya 12ga watan Yuni.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gama shirye-shiryen yin garambawul a majalisar ministocinsa wanda ya haɗa da kirkiro sabuwar ma'aikata da sauke mi istoci.
Yan sanda sun gaza kai sammaci ga Sarki Aminu Bayero da sauran sarakuna hudu da aka tsige wanda hakan ya kawo tsaiko a ci gaba da sauraron shari'ar masarautar Kano.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ce idan aka jingine siyasa aka ɗauki manufa ɗaya za a iya kawo karshen ƴan bindiga a cikin mako biyu kaɗai.
Malam Dikko Umaru Radda ya lashi takobin kawo ƙarshen ƴan bindiga a faɗin jihar Katsina, ya yi ta'aziyyar kisan mutane kusan 30 a yankin ƙaramar hukumar Ƙankara.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bai wa sababbin shugabannin ƙananan hukumomi 17 da mutane suka fito suka zaɓa ranar Asabar, 8 ga watan Yuni.
Tsohon daraktan babban bankin Najeriya, Ahmed Umar ya yi bayanin yadda Emefiele ya shure tsarin sababbin kuɗin da Muhammadu Buhari ya amince da su.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya dakatar da kwamishinar lafiya daga aiki bisa zargin rashin gaskiya da almundahanar kuɗaɗe.
Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara da ake zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi awon gaba da dumbin fasinjoji a kan babban titin Maiduguri zuwa Kano.
Ahmad Yusuf
Samu kari