Bayan APC Ta Samu Galaba, Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Shugabanni 17

Bayan APC Ta Samu Galaba, Gwamna Ya Rantsar da Sababbin Shugabanni 17

  • Gwamna Buni na jihar Yobe ya rantsar da sababbin ciyamomin da suka lashe zaben da aka yi ranar Asabar da ta gabata
  • Mai Mala Buni ya buƙaci sababbin shugabannin da su mayar da hankali wajen taimakon jama'a da tallafawa matasa, mata da masu karamin ƙarfi
  • Buni ya tunatar da su cewa su ne a sahon gaba wajen aiwatar da manufofin gwamnati saboda sun fi kowa kusa da jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya rantsar da sababbi kuma zababbun shugabannin kananan hukumomi 17 na jihar.

Wannan na zuwa ne bayan nasarar da suka samu a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata, 8 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dakatar da kwamishina bayan gano wata baɗaƙala, ya ɗauki mataki

Gwamna Mai Mala Buni.
Shugabannin kananan hukumomin da aka zaɓa a Yobe sun kama aiki Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Mala Buni ya rantsar da sababbin ciyamomin ne a wani biki da aka shirya a fadar gwamnatinsa da ke Damaturu ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Buni ya ja hankalin ciyamomin

Da yake jawabi, Mai Girma Gwamna Buni ya buƙaci ciyamomin su maida hankali wajen yiwa al'umma hidima domin sun fi kusa da talakawa.

Buni ya kuma bukaci shugabannin da su yi amfani da dukiyar yankunansu ta hanyar da ta dace kuma su tabbata ayyukan gwamnati sun amfanar da jama’a.

A cewarsa, zaɓen da aka kammala ya nuna manufar gwamnatinsa na ƙara gina tsarin demokaraɗiyya tun daga matakin farko.

Gwamnan ya ƙara da cewa jam'iyyun siyasa da ƴan takara sun bai wa al'umma damar su zaɓi wanda suka fi aminta da shi.

Mai Mala Buni ya jaddada cewa wannan zaɓen ya kara nuna yadda jama'a ke riƙe da ƙarfin ikon zaɓen shugabanni a hannuwansu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta harzuƙa ƴan jarida, sun dauƙi mataki kan Abba da jami'ansa

Gwamna ya yabawa jam'iyyun siyasa

Buni ya yabawa dukkanin jam’iyyun siyasa, ’yan takara, da magoya bayansu bisa yadda suka nuna kishi wajen gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Ya ce:

"Ina tunatar da ku shugabannin kananan hukumomi cewa ku sani ku ne a sahun gaɓa wajen aiwatar da kyawawan manufofin gwamnatinmu, tallafawa matasa, mata da marasa galihu."

Buni ya yi kira ga ciyamomin da su ji tsoron Allah, su sa gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kudaden gwamnati, kadarori da kayan aiki, Daily Post ta ruwaito.

Tinubu ya sauke shugaban PSC

Kuna da labarin Bola Ahmed Tinubu ya sauke Solomon Arase daga matsayin shugaban hukumar jin daɗin ƴan sanda ta ƙasa (PSC) ranar Litinin, 10 ga watan Yuni

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya ce Tinubu ya naɗa DIG Hashimu Argungu a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262