Boko Haram: 'Yan Ta'adda Sun Tafka Ɓarna, Sun Sace Mutane a Babban Titin Zuwa Kano

Boko Haram: 'Yan Ta'adda Sun Tafka Ɓarna, Sun Sace Mutane a Babban Titin Zuwa Kano

  • Ƴan Boko Haram sun kai farmaki kan matafiya a babban titin Maiduguri zuwa Kano da yammacin ranar Litinin, 10 ga watan Yuni
  • Rahotanni su ce maharan sun toshe bangare ɗaya na titin da ƙarfe 5:50 na yamma, sun tafi da fasinjoji da dama
  • Wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƴan ta'adda sun kawo cikas a babban titin wanda ya saba cika da motoci masu tafiya da masu dawowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rahotannin da muka samu ba da jimawa ba sun nuna cewa wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari babban titin Maiduguri zuwa Kano.

Bayanai sun nuna cewa ƴan ta'addan sun kwashi fasinjoji da dama sun yi awon gaba da su zuwa wurin da ba'a sani ba.

Kara karanta wannan

Bankin CBN ya soke lasisin wasu manyan bankuna 4 a Najeriya? Gaskiya ta fito

Yan sandan Najeriya.
'Yan Boko Haram sun yi garkuwa da matafiya da dama a titin Maiduguri zuwa Kano Hoto: Nigeria Folice Force
Asali: Twitter

Wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Trust cewa maharan sun kai farmakin ne a tsakanin garin Kuturu da Mannanari da ke kan babban titin Maiduguri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya afku ne da misalin ƙarfe 5:50 na yamma ranar Litinin, inda ƴan ta'addan suka toshe titin kafin daga bisani suka tafi da wasu fasinjoji.

Halin da Boko Haram suka jefa matafiya

Harin dai ya sa daruruwan matafiya da masu ababen hawa suka tsaya cirko-cirko a sassa biyu na titin wanda mutane ke yawan bi.

Dole matafiyan suka koma kauyukan Benishek da Auno domin su tsira daga sharrin ƴan ta'addan, cewar rahoton Punch.

"An kai hari tsakanin kauyukan Mannanari da Garin Kuturu, inda wasu mayaƙan Boko Haram suka toshe ɓangaren motoci masu zuwa, suka sace fasinjoji da dama."
"Ba mu da tabbacin yawan mutanen da maharan suka yi garkuwa da su amma babu shakka an sace mutane da yammacin ranar Litinin."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarna, sun tafi da matafiya da yawa a hanyar zuwa Abuja

- Majiya

Mazauna yankin sun ce motocin haya da yawa sun dawo sun fake a cikin ƙauyukansu a lokaci da maharan suka toshe titin.

Sojoji sun kai ɗauki bayan harin B/Haram?

Wani fasinja, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce suna da yawa waɗanda suka maƙale, suna jiran sojojin da suka kawo ɗauki su tsaftace hanyar.

“Muna kan hanyar Kano daga Maiduguri sai direban mu ya samu labarin harin cikin sauri ya yi kwana muka koma."

Yan bindiga sun farmaki titin Abuja

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama yayin da suke hanyar zuwa birnin tarayya Abuja daga jihar Enugu.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya ce lamarin ya faru ne a kan titin Nasarawa-Keffi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262