Shugaba Tinubu Zai Kaddamar da Zane Mafi Girma a Duniya a Ranar Demokuradiyya

Shugaba Tinubu Zai Kaddamar da Zane Mafi Girma a Duniya a Ranar Demokuradiyya

  • Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu za ta kaddamar da zane mafi girma a duniya ranar bikin dimokuraɗiyya
  • Shugaban ƙasa ne zai jagoranci lamarin a wani ɓangare na cikar Najeriya shekara 25 a tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba tare da tangarɗa ba
  • Opeyemi Alaba, wanda ya kirkiro zanen ya bayyana cewa fentin zanen yana wakiltar jihohi 36 da birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Najeriya karƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu za ta kaddamar da hoton zane mafi girma a duniya a ranar dimokuraɗiyya.

Za a kaddamar da zanen a wurin bikin cikar Najeriya shekaru 25 a tsarin mulkin dimokuraɗiyya a babban filin Eagle Square da ke Abuja yau Laraba, 12 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

12 ga Yuni: 'Yar'adua, Abiola da mutane 30 da suka tabbatar da dimokuradiyyar Najeriya

Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta shirya kaddamar da zanen da babu kamarsa a duniya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Zanen shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Opeyemi Alaba, wanda ya ƙirƙiro zanen, ya bayyana shi a matsayin sakon fata nagari ga ‘yan Najeriya da nahiyar Afirka baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta kawo, Mista Alaba ya ce masu zane 37 da suka wakilci jihohi 36 da birnin tarayya Abuja ne suka yi wannan zane da za a ƙaddamar.

Masu zanen dai sun zana hoton Bola Ahmed Tinubu wanda kuma ana ganin zai zama zane mafi girma a duniya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke bikin cika shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya ba tare da katsewa ba, Guardian ta ruwaito.

Meyasa ake murnar ranar dimokuradiyya?

Najeriya dai ta ɗauki shekaru da dama ana mulkin soja ba tare da kundin tsarin mulki ba kafin daga bisani ta koma tsarin dimokuradiyya a 1999.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya bayyana nasara 1 da Najeriya ta samu saboda dimokuraɗiyya

Olusegun Obasanjo ne ya fara mulkin Najeriya bayan dawowar dimokuraɗiyya a 1999 kuma a wannan lokacin aka zaɓi Bola Tinubu a matsayin gwamnan Legas.

Tinubu ya kasance a jam'iyyar adawa tun daga jam'iyyar AD zuwa ADC zuwa ACN, daga baya kuma aka yi haɗakar da ta haifar da APC a zaɓen 2015.

A halin yanzu Tinubu ya fara zangon mulkinsa na farko wanda zai cika shekara 12 da kafa gwamnatin APC idan ya kammala ranar 29 ga watan Mayun, 2027.

Tinubu zai yi garambawul a gwamnatinsa

A wani rahoton Bola Tinubu na shirin yin garambawul a majalisar ministocinsa wanda ya haɗa da korar wasu da kuma naɗa sababbin ministoci a gwamnatinsa.

Ana kuma tsammanin shugaban ƙasar zai kirkiro sabuwar ma'aikatar raya dabbobi domin aiwatar da tsarin kiwo da aka kaddamar a bara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262