Gwamna Ya Dakatar da Kwamishina Bayan Gano Wata Baɗaƙala, Ya Ɗauki Mataki

Gwamna Ya Dakatar da Kwamishina Bayan Gano Wata Baɗaƙala, Ya Ɗauki Mataki

  • Alex Otti na jihar Abia ya dakatar da kwamishinar lafiya ta jihar, Dr. Ngozi Okoronkwo bisa zargi rashin gaskiya da almundahana
  • Wani jami'in gwamnatin Abia ya bayyana cewa Gwamna Otti ya ɗauki matakin ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan zargin da ake yi mata
  • Wannan mataki na zuwa ne kwanaki biyu bayan gwamnatin Abia ta dakatar da shugabar makarantar jinya bisa zargin aikata ba daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Rahotanni sun nuna cewa Alex Otti ya dakatar da kwamishinar lafiya ta jihar Abia, Dokta Ngozi Okoronkwo.

Bayanai sun nuna cewa gwamnan ya dakatar da ita ne bisa zargin rashin gaskiya da kuma almundahanar makudan kudade.

Kara karanta wannan

Kotu ta dawo da basaraken da El-Rufai ya tuge, ta ci tarar gwamnatin Kaduna N10m

Gwamna Alex Otti na jihar Abia.
Gwamma Otti na jihar Abia ya dakatar da Dokta Ngozi daga matsayin kwamishinar lafiya Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Kwamishinar lafiya za ta bar ofis a Abia

A rahoton jaridar Vanguard, an dakatar da kwamishinar har sai baba-ta-gani a wurin taron majalisar zartarwa na jihar Abia ranar Litinin, 10 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani babban jami’in gwamnatin Abia ya tabbatar wa jaridar cewa da gaske ne gwamnan ya umarci kwamishinar lafiya “ta sauka daga muƙamin, ta koma gefe."

Meyasa Gwamna Otti ya dakatar da kwamishinar?

A cewar jami'in wanda ya nemi a sakaya sunansa, gwamna ya ɗauƙi matakin ne domin ya bayar da damar gudanar da bincike kan Dr. Ngozi da ma’aikatarta.

Ya ce:

"Akwai ayar tambaya a yanayin gaskiyarta yayin gudanar da ayyukan da ke kanta kuma gwamna na ganin wasu abubuwan sun saɓawa manufarsa ta yin gaskiya da rikon amana.
"Saboda haka ne ya umarci kwamishinar ta sauka domin a gudanar da bincike a tsanake ba tare da samun cikas ba."

Kara karanta wannan

Bayan APC ta samu galaba, gwamna ya rantsar da sababbin shugabanni 17

A halin da ake ciki dai duk wani kokarin jin ta bakin Kwamishinar ya ci tura domin ba ta amsa kiran da aka yi mata ta wayar tarho ba, rahoton Naija News.

Dakatar da kwamishinar na zuwa ne sa’o’i 48 bayan dakatar da shugabar makarantar koyon aikin jinya, Abiriba, bisa zargin ta da hannu a rashin gaskiya da cin amana.

Gwamna Eno ya tsige kwamishina

Rahoto ya zo cewa Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Eno ya tsige kwamishinan ayyuka na musamman, Bassey Okon daga muƙaminsa, ya umarci ya bar ofis nan take.

Sakataren gwamnatin jihar Akwa Ibom, Prince Enobong Uwah ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, 10 ga watan Yuni, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262