Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019

- Kwallo na da mutukar muhimmanci a wurin al'umma, domin kuwa tana taimakawa matuka wurin debewa mutane kewa

- Akwai 'yan wasan kwallon kafa Musulmi bila adadin a duniya

- Amma munyi kokarin ciro muku guda goma wadanda ake ji dasu a duniyar kwallon kafa

Wasan kwallon kafa na da mutukar muhimmanci a wurin al'umma, kuma akwai manyan 'yan wasan kwallon kafa na duniya da suke bin addinin Musulunci.

Hakan ne ma yasa muka binciko muku wasu fitattun manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmai guda goma a wannan shekarar ta 2019.

Ga jerin 'yan wasan a kasa:

1. Mohammed Salah (Egypt)

Na farko a jerin shine Mohammed Salah, wanda aka fi sani da (Mo Salah), ko kokwanto babu dan wasan kwallon kafa na kungiyar Liverpool shine dan wasan da yafi kowa a cikinsu.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Mohammed Salah (Mo Salah)
Asali: Depositphotos

2. Fahad Al-Muwallad (Saudi Arabia)

Al-Muwallad ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Levante, wacce ke buga wasan La Liga, bayan ya bar tsohuwar kungiyarsa ta Al-Ittihad.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Fahad Al-Muwallad
Asali: Facebook

3. Mehdi Benatia (Morocco)

Dan wasan mai shekaru 31 yana taka leda a kungiyar wasan kwallon kafa ta Juventus ne dake kasar Italy, bayan ya bar kungiyarsa ta Bayern Munich a shekarar 2017.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Mehdi Benatia
Asali: Facebook

4. Sardar Azmoun (Iran)

Mutane da yawa basu san wannan dan wasan ba mai shekaru 23, saboda baya taka leda a yankin Turai. Sadar Azmoun yana taka leda ne a kungiyar wasa ta Rubin Kazan dake kasar Russia.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Sardar Azmoun
Asali: Facebook

5. Paul Pogba (France)

Pogba ya bar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a shekarar 2012, inda ya tafi kungiyar Juventus, sannan ya kara dawowa Manchester a shekarar 2016 akan kudi fam miliyan 89.3.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Paul Pogba
Asali: Getty Images

6. Ahmed Musa (Nigeria)

Dan wasan Najeriyan ya yiwa kungiyar shi ta Najeriya kokari mutuka a wasan kwallon kafa da aka yi na duniya a shekarar 2018, a kasar Russia.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Ahmed Musa
Asali: Getty Images

7. Xherdan Shaqiri (Switzerland)

Shaqiri dan asalin kasar Switzerland ne, kuma yayi wasanni masu yawa a kungiyoyin kwallon kafa na Turai.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Shaqiri
Asali: Getty Images

8. Mesut Ozil (Germany)

Ozil wanda yake bugawa kasar Germany wasa, yayi murabus daga bugawa kasar wasa a shekarar 2014. Dan wasan Arsenal din, ya yiwa kungiyar tasa kokari matuka.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Mesut Ozil
Asali: Getty Images

9. Marouane Fellaini (Belgium)

Yana da sauki a gano shi a cikin fili, saboda yanda yanayin gashinsa yake. Dan wasan mai shekaru 30 a duniya yayi suna a bangaren kungiyarsa dama kasar sa baki daya.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Marouane Fellaini
Asali: UGC

10. Sadio Mane (Senegal)

Musulmin dan wasa na karshe a jerin shine Sadio Mane. Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool yana wasa tare da takwaransa, Mohammed Salah. Shi da Salah suna buga wasa fiye da tunanin mutum idan suka hadu.

Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Wasanni: Jerin manyan 'yan wasan kwallon kafa Musulmi guda 10 a shekarar 2019
Asali: Getty Images

Wannan mun tsakuro muku kadan daga cikin 'yan wasan kwallon kafa Musulmi ne, akwai su bila adadin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng