Real Madrid vs Arsenal: Rigima Ta Barke tsakanin Matasa a Kano kan Wasan UCL
- Rikici ya barke a karamar hukumar Fagge da ke Kano, bayan wasan kusa da na kusa da na karshe tsakanin Arsenal da Real Madrid
- Magoya bayan Real Madrid sun fusata da rashin nasarar su 2-1, inda Arsenal ta samu nasara da ci 5-1 jimilla a wasannin gasar Turai
- Wani bidiyo ya bayyana yadda matasa suka rika jifa da duwatsu, ana fada da ihu a tsakanin magoya bayan kungiyoyin na Ingila da Sifen
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Fagge, Kano - Tashe-tashen hankula sun barke a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano yayin da magoya bayan kwallon kafa suka yi fada.
Fadan ya biyo bayan rashin nasarar Real Madrid da ci 2-1 a hannun kungiyar Arsenal, wanda ya sa 'Gunners' suka samu nasara jimilla da ci 5-1.

Asali: Facebook
Bidiyon matasa na rigimar Madrid/Arsenal a Kano
Wani faifan bidiyo da Mustapha Muhd Gujba Banker ya saka a Facebook ya nuna yadda suka rika duka, jifa da duwatsu da hayaniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan sakamakon ya janyo fushin wasu magoya bayan Real Madrid, inda suka shiga fada da masu murna daga bangaren Arsenal.
Lamarin ya faru ne a daren jiya Laraba 16 ga watan Afrilun 2025 jim kadan bayan tashi daga wasan Real Madrid da Arsenal.
Sakon da aka saka a bidiyon ya bayyana cewa fadan ya barke ne bayan tashi daga wasa, inda sabani ya rikide zuwa rikici.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba har zuwa safiyar yau Alhamis game da abin da ya faru.
Har yanzu ba a tabbatar da kama kowa ba ko kuma samun wanda ya ji rauni yayin fadan da ya barke tsakanin magoya bayan.

Asali: Original
Wasu masu ta'ammali da kafofin sadarwa sun yi martani kan bidiyon da aka wallafa na rigima tsakanin matasa a Kano.
Daga cikin wadanda suka yi martani akwai wadanda ke ganin bai kamata kwallo ta haddasa fada ba.
Wasu ko sukar yan Kano suke yi da cewa komai a wurinsu na fada ne hatta abin da bai kamata a yi fada a kai ba.
Martanin mutane kan rigimar wasan Madrid-Arsenal
Abdullahi Ibrahim:
"Allah na gode ma da ba na kallon kwallo, idan kana neman wanda ba shi da hankali duk matakin karatunsa idan ka samu kallon kwallo to shi ne."
MH Mustapha Bamami:
"A Kano komai abin fada ne a gurinsu."
Khalid Umar:
"Su Kanawa jahilcinsu kullum karuwa yake, me ya haɗa kwallo da fada kuma."
Ɗan daba ya mika wuya ga yan sandan Kano
Mun ba ku labarin cewa wani matashi dan shekara 20, Umar Auwal, ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan Kano tare da amsa laifin kashe mutane da dama a Kano da Jigawa.
Matashin ya bayyana yadda ya kashe mutane a Sabon Gari da Kurna a jhar Kano da kuma Ringim a Jigawa, yana sace wayoyi da babura.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori PhD, ya yi kira ga sauran masu laifi su tuba domin ba za su samu mafaka ba a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng