Ballon d'Or: Ronaldo Ya Bar Kame Kame, Ya Faɗi Wanda Ya Cancanci Lashe Kyautar a Bana

Ballon d'Or: Ronaldo Ya Bar Kame Kame, Ya Faɗi Wanda Ya Cancanci Lashe Kyautar a Bana

  • Fitaccen dan wasan ƙwallon ƙafa, Cristiano Ronaldo ya fadi wanda ya kamata a ba kyautar Ballon d'Or a kakar wasa ta bana
  • Ousman Dembele da Lamine Yamal suna cikin wadanda ake ganin sun cancanta, yayin da Yamal ke haskawa a wasanni
  • Ronaldo ya ce ba zai iya cewa ko wanene ya fi cancanta a bana ba amma ya fadi tsarin da ya kamata a riƙa bi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Munich, Germany - Shahararren dan wasan kwallon kafa a duniya, Cristiano Ronaldo ya magantu kan kyautar Ballon d'Or da ake bayarwa kowace shekara.

Ronaldo wanda ya lashe kyautar har sau biyar ya fadi wanda ya kamata a ba kyautar a bana.

Ronaldo ya yi magana kan Ballon d'Or
Ronaldo ya fadi wanda ya kamaci lashe Ballon d'Or. Hoto: Cristiano Ronaldo, France Football.
Asali: Facebook

Matsayar Ronaldo kan kyautar Ballon d'Or

Hakan na cikin wata sanarwa da fitaccen dan jarida a harkar wasanni, Fabrizio Romano ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ronaldo ya bayyana haka ne yayin hira da yan jaridu gabannin wasan karshe na gasar 'Nations League' tsakanin Spain da Portugal.

'Dan wasan ya ce ba wanda ya lashe gasar 'Champions League' wannan gagarumar kyauta shi ne ya fi dacewa.

Da yake magana gabanin wasan karshe, ya ce “kofuna” ne ya kamata su kayyade wanda zai ci Ballon d'Or.

“A gani na, wanda ya kamata ya ci, ya kamata ya kasance a cikin ƙungiyar da ta ci kofuna, wanda ya lashe gasar zakarun Turai shi ya kamata a ba kyautar Ballon d'Or."

- Cewar Cristiano Ronaldo

An fara hasashen wanda zai lashe kyautar Ballon d'Or
Ronaldo ya fadi matsayarsa kan kyautar Ballon d'Or. Hoto: France Football.
Asali: Getty Images

Hasashen da ake yi kan kyautar Ballon d'Or

An fara bayar da kyautar Ballon d’Or a shekarar 1956 ta mujallar 'France Football' ga ɗan wasan da aka fi ganin ya fi kowa a kakar da ta gabata.

PSG ta lallasa Inter Milan 5-0 a wasan karshe na Champions League, hakan ya kara karfafa kira ga a ba Ousman Dembele kyautar Ballon d’Or na bana.

Sai dai wasan Lamine Yamal da ya haskaka a nasarar 5-4 da suka samu a kan Faransa a wasansu a gasar 'Nations League' ya jawo cece-kuce.

Wasu na ganin ya kamata a ba Yamal kyautar, wanda zai sa ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa lashe Ballon d'Or a tarihi.

Ronaldo da Messi sun mamaye kyautar na tsawon shekara goma daga 2008 zuwa 2017. Yanzu haka Rodri na Spain da Man City ne ke rike da ita.

Tattaunawar Legit Hausa da masoyin kwallon kafa

Wani mai goyon bayan kungiyar Barcelona ya soki kalaman Cristiano Ronaldo kan kyautar Ballon d'Or.

Matashin da ake cewa Adamu Messi ya ce shi kansa Ronaldo ya taba cin kyautar Ballon d'Or ba tare da lashe gasar zakarun Turai ba.

Ya ce:

"Ba za mu manta ba a 2013 an yi wa Ribery kwace wanda shi ne ya ci gasar zakarun Turai amma aka ba Ronaldo da bai ci komai ba."

'Yan wasan da za su iya lashe Ballon d'Or

Mun ba ku labarin cewa kungiyar kwallon kafa ta PSG ta samu nasarar lashe gasar zakarun nahiyar turai, lamarin da ya jawo sabuwar muhawara kan kyautar Ballon d'Or ta 2025.

Bayan kakar wasa mai ban mamaki da ya yi, tauraron PSG, Ousmane Dembele ya shiga gaba a manyan ‘yan wasan da ake ganin za su lashe wannan kambu.

Ɗan wasan Barcelona Lamine Yamal, wanda ake kallonsa a matsayin magajin Lionel Messi, shi ma yana cikin waɗanda ake ganin za su iya lashe Ballon d'Or.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.