Ronaldo Ya Jefa Duniya a Rudani kan Shirin Barin Al Nassr Ta Saudiyya
- Cristiano Ronaldo ya jefa duniya cikin rudani kan shirin cewa zai bar Al Nassr bayan ya wallafa sako a kafafen sada zumunta
- Ya rubuta cewa “An rufe wannan babi' a wani sako da ya fitar wanda ke nuni da yiwuwar kammala zaman sa a kulob ɗin Saudiyya
- Rahotanni na cewa Al Nassr ta rasa damar shiga gasar zakarun Asiya bayan shan kashi 3-2 a hannun Al Fateh a wasansu na ƙarshe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Shahararren ɗan kwallon ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya jefa masoya wasanni da masharhanta cikin rudani kan wani sako da ya wallafa.
Sakon da ya wallafa ya nuna cewa akwai alamar zai bar Al Nassr da yake takawa leda a kasar Saudiyya.

Asali: Getty Images
Legit ta tattaro bayanin da Ronaldo ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a daren Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sakon, Ronaldo ya ce:
"An rufe wannan babi. Na gode da kwarai,”
Masu sharhi na cewa hakan na nuni da wani sabon mataki a rayuwarsa ta wasanni, yayin da kwantiraginsa da kulob ɗin Al Nassr ke dab da ƙarewa a ƙarshen wannan kakar.
Ana ganin cewa sakon Ronaldo na da nasaba da rashin nasarar Al Nassr a wasansu na ƙarshe da Al Fateh, wanda ya hana su samun gurbin gasar zakarun Asiya.
Ronaldo ya kusa cin kwallaye 100
Ronaldo ya ci kwallonsa ta 25 a kakar bana a wasan da suka yi da Al Fateh, wanda ya kai adadin kwallayensa da Al Nassr zuwa 99 cikin wasanni 111 da ya bugawa kulob ɗin.
Sai dai duk da hakan, ba su samu nasara ba, inda suka sha kashi 3-2 a hannun Al Fateh a yayin wasan.
Wannan mummunan sakamako ya sa Al Nassr ta kasa kammala kakar da damar shiga manyan gasa na nahiyar Asiya, lamarin da ya ƙara haifar da jita-jitar barin Ronaldo.

Asali: Getty Images
A cikin shekarun da Ronaldo ya shafe da Al Nassr, kulob ɗin bai samu lashe wani kofi ba duk da irin nasarorin da ya samu na ƙashin kansa.
Batun makomar Ronaldo a kwallon kafa
Rahotanni sun nuna cewa tattaunawa kan sabon kwantiragi tsakanin Ronaldo da Al Nassr sun tsaya cak, kuma ɗan wasan na dab da zama ɗan wasa mai 'yanci yayin bazara.
Shafi mai sharhi kan wasanni na Goal ya wallafa cewa Ronaldo ya sha bayyana cewa ba zai yi ritaya ba har sai ya kai ga cin kwallaye 1,000, inda yanzu ya cika 940.
Wannan na nuni da cewa har yanzu yana da sha’awar ci gaba da buga ƙwallo a wani kulob, ko na Turai ko na wata ƙasa.
Ko da yake bai bayyana inda zai nufa ba tukuna, an dai saba da Ronaldo yana amfani da irin wannan harshe idan zai sauya kulob ko shiga sabon mataki.
Ronaldo ya ce ya fi kowa iya kwallo
A wani rahoton, kun ji cewa Cristiano Ronaldo ya ce ya fi kowa iya taka leda a fadin duniya a yanzu haka.
Ronaldo ya ce babu tantama a kan abin da ya fada domin nasarorin da ya samu a kwallon kafa sun tabbatar da hakan.
Shaharren dan kwallon ya kuma bayyana dalilin da ya hana shi data leda a Barcelona duk da sharar da kulob din ta yi a duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng