WC 2022: Abin da Tinubu, Atiku da Kwankwaso Suka Fada kan Argentina, Messi

WC 2022: Abin da Tinubu, Atiku da Kwankwaso Suka Fada kan Argentina, Messi

  • ‘Yan takaran kujerar shugaban kasa a Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu a kan gasar kofin kasashen Duniya
  • Atiku Abubakar ya ce akwai darasin da za a dauka a rayuwar Lionel Messi da ya jagoranci kasar Argentina
  • Kamar yadda Bola Tinubu yake ikirarin zaben 2023 lokacinsa ne, ‘dan takaran yace lokacin Messi ne a Doha

Qatar - Duniya duk ta amsa yayin da kasar Argentina ta lashe gasar cin kofin Duniya a karon farko bayan sama da shekaru 35.

Magoya bayan Lionel Messi su na ta farin ciki ganin gwarzonsu ya lashe gasar da ya yi shekara da shekaru yana nema a rayuwarsa.

Abin bai kare kan magoya bayan Lionel Messi ba, Atiku Abubakar mai neman mulkin Najeriya a 2023, ya taya Argentina murna.

‘Dan takaran kujerar shugaban kasar da yake magana a shafinsa na Twitter, ya ce za a koyi darasi daga rayuwar Lionel Messi.

Kara karanta wannan

Tinubu ga 'yan Kaduna: Ni na san yadda zan kawo karshe 'yan bindiga, ku zabe ni na gaji Buhari

Nasarar Lionel Messi bayan ya yi ritaya

A 2016, Messi ya yi ritaya daga bugawa kasarsa kwallo, a sakamakon rashin nasarar da Argentina ta samu a gasar Copa America.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shekaru shida da dawowa bugawa Argentina, sai Messi ya lashe gasar kwallon da ta fi kowace.

Argentina
Argetina ta ci gasar kofin Duniya Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC
“Ina taya Argentina murna. Messi zai nuna maka cewa ka da ka karaya a ko wani irin yanayi ka samu kan ka. Ya bar mafi kyawun a lokacin karshe. -AA #ARGFRA #FIFAWorldCup

- Atiku Abubakar

‘Emi lo kan’

Shi kuma ‘Dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu, ya kamanta Lionel Messi ne da shi kan sa.

Kamar yadda Tinubu yake yi wa kansa take da ‘Emi lo kan’, watau wanda lokacinsa ya yi da zai mulki Najeriya, ya ce haka Messi yake.

Kara karanta wannan

Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Zabensa na 2023 a Borno

Tinubu ya daura hoton Tauraron yayin da aka yi masa kwaskwarima da irin hularsa, ya ce shi ne ‘Emi lo kan’ na Doha da ke kasar Qatar.

Gasa tayi kyau - Kwankwaso

Shi Rabiu Kwankwaso mai neman shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP cewa ya yi karshen gasar kofin Duniyan na 2022 ya yi armashi.

A jawabin da ya yi a Twitter a ranar Lahadi, Rabiu Kwankwaso ya taya kasar Argentina murnar nasararta a kan kasar Faransa.

Aliyu Mukaddas ya ce ‘dan takaran na NNPP ya jinjinawa gwarzon Duniya watau Lionel Messi da daukacin ‘yan wasan kasar Argentina.

Shi dai wannan Aliyu Mukaddas ne yake cewa Tinubu ya ba shi dariya da ya jinjinawa Messi, ya ce jiya ranar farin cikin ‘dan wasan ne.

Zakarun Qatar 2022

Kamar yadda rahoto ya zo dazu, Emilliano Martinez ne ya samu kyautar mai tsaron gidan da ya fi kowa kokari a gasar cin kofin Duniya.

Kara karanta wannan

Saura Kiris: Yadda Su Atiku Abubakar Suka Kusa Aika Ni Barzahu - Kakakin Takarar Tinubu

Enzo Fernandez shi ne gwarzon matashin 'dan wasa, Kyllian Mbappe kuma ya fi kowa kwallaye, sai Lionel Messi shi ne gwarzon gasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel