Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Tazarcensa, Buratai da Modu Sheriff Suna Bayansa

Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Tazarcensa, Buratai da Modu Sheriff Suna Bayansa

  • Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da yakin neman tazarcensa a cikin dubban magoya bayansa da masu ruwa da tsakin APC
  • Zulum a yayin gagarumin taron da aka yi a filin wasa na Ramat, ya sanar da yadda ya inganta tsaro a jihar tare da durkusar da Boko Haram
  • Ya sha alwashin dasawa daga inda ya tsaya matukar aka zabeshi yayin da ya samu goyon bayan Ali Modu Sheriff da Tukur Buratai

Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya kaddamar da yakin neman zabensa na 2023 inda yace yanzu Borno ta zama jiha mai lumana da kwanciyar hankali, jaridar Vanguard ta rahoto.

Gwamna Zulum na Borno
Zulum ya Kaddamar da Yakin Neman Tazarcensa, Buratai da Modu Sheriff Suna Bayansa. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

Wannnan na zuwa ne bayan tsohon shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai da manyan ‘yan siyasar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, suka bayyana goyon bayansu kan tazarcen Gwamnan inda suka kwatanta shi da Gwamnan da yafi kowanne aiki a tarihin jihar.

Kara karanta wannan

Gombe: ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari, Sun Kone Amfanin Gona Tare da Halaka Mutum 3

Yayin jawabi wurin ralin kaddamar da kamfen dinsa a filin wasa na Ramat dake Maiduguri a ranar Litinin cikin dandalin jama’a da suka hada da magoya bayansa da masu ruwa da tsarin APC, Zulum ya jaddada cewa a yanzu Borno lafiya kalau take kuma kwanakin farmakin Boko Haram sun shude a karkashin mulkinsa.

Kamar yadda yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A karon farko a tarihi, babu rahoton hari ko garkuwa da mutane na Boko Haram a kowacce karamar hukumar a jihar.
“A yanzu dubban mayakan ta’addanci na Boko Haram suna mika wuya ga sojoji, mun mayar da ‘yan gudun hijira miliyan daya gidajensu, mun mayar da hankali wurin dawo da zaman lafiya da tsaro a dukkan Borno saboda muna nasara a yaki da Boko Haram.
“Mulkina ya mayar da hankali wurin bayar da cikakken tsaro ga jama’a kuma muna fatan dawo da hada-hadar kawuwancinmu zuwa karshen 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

“Muna aiki da jami’an tsaro wurin dawo da tafiyar dare daga Maiduguri zuwa Damaturu da kuma daga Maiduguri zuwa dukkan kananan hukumomin jihar 27.”

- Zulum yace.

Yayi alkawarin tabbatar da karin karfin jami’an CJTF, mafarauta da ‘yan sa kai domin karfafa tsaro a Borno.

Zulum yayi kira ga masu ruwa da tsaki da magoya bayan jam’iyyar da su cigaba da goyon bayan gwamnatinsa da addu’o’i domin cika alkawurran kamfen dinsa.

Buratai da Modu Sheriff sun bayyana goyon bayansu

A yayin bayyana gamsuwarsa kan hadin kan da mambobin jam’iyyar suka nuna yayin kaddamar da kamfen dinsa, yayi kira garesu da su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar APC a zaben 2023.

A daya bangaren, tsohon shugaban rundunar sojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Buratai mai ritaya da Sanata Ali Modu Sheriff, sun bayyana goyon bayansu kan kudirin tazarcen Gwamna Zulum.

Sun yi jawabi a yayin kaddamar da kamfen din a ranar Litinin, 12 ga watan Disamban 2022.

Dukkansu sun yi bayani kan shugabancin jihar a shekaru 20 da suka gabata inda suka yabawa Farfesa Zulum saboda aikin da yayi fiye da gwamnonin farar hula hudu da aka taba yi a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel