Saura Kiris: Yadda Su Atiku Abubakar Suka Kusa Aika Ni Barzahu - Kakakin Takarar Tinubu

Saura Kiris: Yadda Su Atiku Abubakar Suka Kusa Aika Ni Barzahu - Kakakin Takarar Tinubu

  • Bayo Onanuga yace yana tafiya sai wata mota a ayarin Atiku Abubakar ta buge shi, tayi masa barna
  • Kakakin na kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu ya bi motar har zuwa wani katafaren gida a Abuja
  • A karshe ya fahimci inda ya kai kansa, kuma aka yi dace wani Hadimin ‘dan takaran ya saurare shi

Abuja - Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga ya tsallake rijiya da baya-baya.

Da yake bada labarin a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 11 ga watan Disamba 2022, Bayo Onanuga yace saura kiris ya mutu a wani hadari.

Onanuga yake cewa tawagar motocin ‘dan takaran PDP na shugaban kasa, Atiku Abubakar ta latse motarsa yayin da yake tafiya a kan hanya.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben na APC yake cewa wannan hadari ya auku ne a babban titin Shehu Shagari a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ina Tinubu Ya Ga Kafasitin Da Zai Mulki Nigeria, Yaje Ya Huta Kawai Inji PDP

Ziyarar Sanata Afikuyomi ta zo da tsautsayi

Rahoton Vanguard yace an latse motar Mista Onanuga a hanyarsa ta komawa gidansa bayan ya dawo daga ziyartar Sanata Tokunbo Afikuyomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar yace yana motarsa Toyota Camry, sai ya hango ayarin motoci a guje, hakan ta sa ya rage gudu, kwatsam sai wata mota ta duro masa.

Atiku Abubakar
Tawagar Atiku Abubakar Hoto: Hoto:www.nairaland.com
Asali: UGC

A cewar tsohon ‘dan jaridar, direban wannan Toyota SUV da ya zo bai tsaya ko ina ba sai ya gwabje motarsa, amma aka yi dace bangaren direba ya buga.

Kamar yadda za a iya gani a wasu hotunan da aka wallafa jiya a dandalin Facebook, a dalilin haka, aka yi wa jikin motar da kuma madubin gefe barna.

Direban da ya yi barna bai tsaya ba

A maimakon motar da tayi barnar ta tsaya domin ganin halin da Bayo Onanuga yake ciki, a cewarsa sai direban ya yi tafiyarsa, shi kuma sai ya bi shi.

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Takara a APC da Sake Neman Mulki

Kamar yadda za a iya gani a wasu hotunan da aka wallafa jiya a dandalin Facebook, a dalilin haka, aka yi wa jikin motar da kuma madubin gefe barna

Daga nan ne jagoran na APC ya samu kan shi a wani katafaren gida a Asokoro, amma ko da isarsa, sai masu gadin gidan suka ce bai isa ya shiga ciki ba.

Bayan ya nuna ayarin motocin mai gidan sun yi masa barna, hakan ya jawo hayaniya har wani Hadimi ya zo, ya yi alkawarin gyara masa motar.

A labarin da ya bada, Onanuga yace ya ga fastocin Atiku/Okowa, da ya tambaya sai aka fada masa gidan ‘dan takaran shugaban kasa a PDP ya shiga.

CBN bai yi tunani ba - Jam'iyyu

Takaita kudin za a cire a banki zai nakasa jam'iyyu da 'yan takara wajen samun kudin kamfe. Rahoto yace jam’iyyun siyasa sun fara wannan kuka.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Babban Abin da Yake Sa Jami'ai Tafka Sata a Gwamnati

Wani jigo a PDP, ‘Dan takaran Shugaban Kasa Jam’iyyar SDP da Kakakin SDP na kasa sun nuna ba su goyon bayan tsarin da Gwamnan CBN ya fito da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel