Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

  • Daya daga cikin manyan ‘yan kwallon kafan Najeriya, Victor Osimhen ya bayar da labarin rayuwar sa ta baya
  • Kamar yadda ya ce, da ba ya da komai har gyaran kwata ya yi wa mutane ana ba shi N20 a matsayin sana’a
  • Dan kwallon mai shekaru 22 ya bayyana yadda ya ke da jajircewa da dagewa wurin tallafa wa iyayen sa

Dan wasan kwallon kafa na Super Eagles na Najeriya da ya fi ko wanne tsada, Victor Osimhen mai shekaru 22 ya bayar da labarin yadda rayuwar sa ta canja cikin shekaru kadan da su ka shude.

Osimhen ya bayyana yadda ya yi kananun sana’o’i kamar gyaran kwata da diban ruwa don samun abinda zai kai bakin salatin sa.

Kara karanta wannan

Buhari ya fusata da halin 'yan bindiga: Yanzu kam kwanakinku sun kusa karewa

Na yi gyaran kwata ana biya na N20, Ɗan Ƙwallon Super Eagles, Osimhem
Dan Kwallon Super Eagles, Victor Osimhen. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A halin yanzu Osimhen ya jefa wa kungiyarsa ta Napoli kwallo biyar a wasanni shida da ya buga.

Matashin dan wasan ya bayyana cewa a baya yana wanke wa mai gidan hayarsu kwata yana biyansa N20 da wasu ayyukan na karfi kamar yadda GOAL ta ruwaito ya furta yayin hira da Head Topics.

Abinda Victor Osimhen ya ce

Tauraron dan kwallon ya ce:

"Na tuna lokacin ina yaro, na kan wanke wa mai gidan hayar mu kwata ya biya ni N20, kuma na kan yi wa makwabtan mu wasu ayyukan karfi kamar diban ruwa a biya ni N80.
"Na yi wannan ayyukan cikin farin ciki domin na yi imanin idan na yi aiki tukuru na samu kudi, zan yi takatsantsan wurin kashe kudin kuma zan taimakawa 'yan uwa na."

Kara karanta wannan

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Ya cigaba da cewa:

"A lokacin da muke tasowa, dan uwa na yana sayar da jarida, yar uwa ta tana sayar da lemu, na kuma ina sayar da ruwa a titi, wasu lokutan sai na yi gudu kafin in karbi kudi daga hannnun matafiya. Ina ganin gwagwarmayar ya taimaka min a rayuwa."

Osimhem ya ce yana yi wa Allah godiya bisa gwagwarmayar da ya yi a rayuwa domin hakan ya taimaka masa zama mutum a yanzu.

A halin yanzu, tsohon dan wasan na Wolfsburg shine dan wasa mafi tsada a nahiyar Afirka bayan siyansa da aka yi a Napoli a bara kuma shine mai jefa kwallo da tauraronsa ke haskawa a Nigeria a yanzu.

Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter

A wani rahoton, wasu masoya, Ameenu da Yetunde, sun bayyana wa mutane yadda su ka hadu har soyayyar su ta kai su ga aure a kafar sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

Kamar yadda Ameenu ya wallafa wani hoto bisa ruwayar Legit.ng, inda ya nuna yadda hirar su ta kasance bayan lokacin da ya tura wa Yetunde sako a 2018.

Ameenu ya bayyana yadda ya fara ne da gabatar wa da Yetunde kan sa bayan ya tambayi yadda take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel