Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter

Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter

  • Yan Najeriya da dama sun sha mamaki akan labarin auren wasu masoya da su ka hadu a kafar sada zumunta
  • Kamar yadda matar ta bayyana, a shekarar 2018 ne Angon, Ameenu ya tura wa Yetunde sako
  • Cikin mintoci 24 ta amsa masa su ka fara hira, daga nan su ka fara gina soyayyar su, ga shi lokacin auren su ya yi

Wasu masoya, Ameenu da Yetunde, sun bayyana wa mutane yadda su ka hadu har soyayyar su ta kai su ga aure a kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda Ameenu ya wallafa wani hoto bisa ruwayar Legit.ng, inda ya nuna yadda hirar su ta kasance bayan lokacin da ya tura wa Yetunde sako a 2018.

Hotunan bikin su, cikin mintuna 24 da tura mata sako ta ba shi amsa
Ameenu da Yetunde. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Ameenu ya bayyana yadda ya fara ne da gabatar wa da Yetunde kan sa bayan ya tambayi yadda take.

A cewar sa, ya sanar da ita yadda ya dauki tsawon lokaci yana lura da wallafar ta a kafar sada zumuntar.

Kamar yadda ya wallafa hoton hirar ta su, bayan ya tura mata sako da mintoci 24 ta amsa masa sannan hira ta tsinke tsakanin su har ta kai ga aure.

Yanzu haka su na sa ran za su ci gaba da rayuwar su ta har abada tare cikin soyayya.

Mutane da dama sun yita tsokaci iri-iri

Bayan wallafar ne ‘yan Najeriya fiye da mutane 200 su ka taru a karkashin wallafar su na tsokaci akan yadda soyayyar ta su ta kasan ce.

Kamar yadda Legit.ng ta bayyana wasu daga cikin tsokacin da mutane su ka dinga tururuwar yi a karkashin wallafar:

Wani Akinwale Omotayo Ezekiel ya ce:

“Na tabbata budurwar ba ta bukaci ya tura mata N2000 cikin gaggawa ba. Da tuni saurayin ya tsere, ina taya ku murna.”

Joseph Okoshone kuwa cewa ya yi:

“Daga baya kuma matar ba za ta taba barin wayar sa ta huta ba, bayan sannin yadda su ka hadu tun farko.”

Rosemary Ezeamadi ta ce:

“Kunga yadda ya gabatar da kan sa a gare ta koh? Babu wasu surutai ba."

Da sauran tsokaci iri-iri daga mutane daban-daban.

Dole ciki ya sa ki saduda da rayuwa, hotunan yadda juna biyu ya sauya wa wasu mata hallita

A wani labarin, Mata da dama su na fuskantar canji a jikin su yayin da suke dauke da juna biyu, wasu su na yin haske yayin da wasu suke yin duhu kwarai.

Akwai wadanda suke yin kiba sosai wasu kuma su rame. Akwai matan da suke yin kyau ko a fuska yayin da wasu kuma kureje suke bayyana musu duk su canja.

Mata da dama sun yi ta wallafa hotunan yadda ciki ya mayar da su, ciki har da fitattun jaruman fina-finai kamar yadda suka wallafa a shafukansu na instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel