Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin

  • Wani matashin dan achaba ya sha yabo tare da samun tukuici mai tsoka bayan ya mayar da wasu makuden kudi da ya tsinta a titi
  • Emmanuel Tuloe ya ji sanarwa inda ake cigiyar makuden kudin a gidan rediyo kuma ya kira tare da mayarwa da masu shi
  • A sakamakon wannan nagarta da gaskiya da ya nuna, an ba shi tukuicin kudi har $1,500 wanda ya yi daidai da N616,350

A wata wallafa da BBC ta yi a ranar 13 ga watan Oktoba, ta ruwaito yadda wani matashi mai suna Emmanuel Tuloe ya mayar da kudi har £37,000 (N20,881,048.40) wanda ya tsinta a babban titi.

Rahoton da aka wallafa ya sanar da yadda Emmanuel ya ga kudin a wata jakar leda kuma ya dauka daga titin.

Kara karanta wannan

Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa

Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin
Dan achaba ya tsinta N20.8m a titi, ya samu tukuicin N600k bayan ya mayar wa masu kudin. Hoto daga Robert/Flickr
Asali: UGC

Babu dadewa kuwa ya ji sanarwa ana cigiyar wadannan makuden kudi a gidan rediyo kuma ya mayar da su.

Matashin ya kira mai kudin kuma ya sanar da ita cewa shi ne ya tsinta kudin a babbar hanya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A matsayin hanyar yabawa da jinjina ga dan achaban, mai kudin ta bai wa Emmanuel kyautar $1,500 (N616,350).

Tuni dai Emmanuel ya zama abun jinjinawa da yabawa a cikin al'umma, BBC ta ruwaito.

Kamar yadda ya wallafa:

"Ya dauka 'yan kasuwan a kan hanyarsu ta zuwa Dengi siyan shanu daga Corona a yankin Yanshanu a Jos. Bayan sun hau Keken a Dilimi, sun samu abun hawa a Dengi sai suka sauka inda suka bar jakar kudinsu a keken."

Direba ya mayar wa 'yan kasuwa N500,000 da suka manta da ita a Kekensa

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

A wani labari na daban, wani matukin Keke ta haya mai suna Mallam Tulu, ya mayar da kudi har N500,000 zuwa ga wasu 'yan kasuwa bayan sun manta da shi a abun hawansa a Jos, jihar Filato.

Kamar yadda wani Bello Lukman na Unity FM Jos ya wallafa a shafinsa na Facebook, 'yan kasuwan su na kan hanyarsu ta zuwa siyan shanu a yankin Yanshanu da ke Jos a ranar Asabar, 16 Oktoba yayin da suka manta da kudin.

"Allah ya albarkaci Mallam Tulu, matukin Keke wanda ya dawo wa da fasinjojin 'yan kasuwa kudi har dubu dari biyar da suka manta da su a Kekensa a Jos," ya ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng