Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya

  • Matsalar tsaro a Najeriya na kara cigaba da ruruwa duk da kokarin da gwamnati ke cewa tana yi don kawo karshen lamarin
  • Rahoto ya nuna cewa a makon da ya gabata kaɗai, yan bindiga sun hallaka aƙalla mutum 31 a hare-hare daban-daban
  • Sai dai masana na ganin kisan jami'an tsaro da mahara ke yi ba shi da alaƙa da rashin makamai, sai rashin sanin makamar aiki

Abuja - Yayin da matsalar tsaro ke ƙara yawaita a Najeriya, aƙalla mutum 31 ne suka rasa rayukansu a hare-hare daban-daban na yan bindiga a faɗin Najeriya makon da ya gabata.

A rahoton da Premium Times ta tattara, ya nuna cewa waɗanda abun ya shafa sun haɗa da dakarun soji 10 da mutanen da basu ji ba basu gani ba 21.

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

Wannan rahoton ya kammalu ne ta hanyar haɗa rahotannin kafafen watsa labarai na harin yan bindiga, saboda haka adadin bai shafi harin da ba'a buga shi ba.

Dakarun sojin Najeriya
Rahoto: Sojoji 10 da wasu mutum 21 sun mutu a harin yan bindiga cikin mako ɗaya a Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin an samu raguwa ne ko karuwa?

Adadin waɗanda suka mutu a makon da ya gabata, ya ragu idan a ka kwatanta shi da na makon da ya shuɗe kafin wannan, inda mutum 41 suka rasa rayukansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a ɓangaren jami'an tsaro kuma an samu ƙaruwar adadin waɗanda suka rasa rayukansu fiye da na makon da ya wuce kafin wannan.

Mafi yawancin kashe-kashen sun auku ne a yankin arewa maso yamma, inda yan bindiga ke cigaba da ayyukan ta'addanci.

Ko meke kawo yawan kashe jami'an tsaro?

Da yake maratani kan lamarin, wani masanin tsaro, Timothy Avele, yace dalilin yawaitar hallaka jami'an tsaro ba shi da nasaba da rashin makamai, sai dai rashin sanin makamr aiki.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Yace:

"Abun takaici ne yanda yan ta'adda, yan bindiga da yan fashi suke hallaka jami'an tsaro, sam wannan ba abune mai kyau ba."
"Ɗaya daga cikin dalilan da yasa hakan ke cigaba da faruwa shine rashin dabaru da kuma rashin sanin makamar aiki, ba wai rashin kayan aiki bane."
"Daga abinda na fahimta, zaka ga jami'in tsaro yana kan bakin aiki amma abinda yafi maida hankali shine kuɗin da zai karba hannun direbobi."

A wani labarin kuma Hukumar Kwastam ta fallasa yadda yan sumogan shinkafa ke tallafawa yan bindiga a Katsina

Shugaban hukumar, Wada Chedi, yace da farko sun fara samun bayanan sirri amma daga bisani suka bi diddigin lamarin har suka tabbatar.

A cewarsa yan sumoga na ƙara wa tankin mai girma sannan su cikashi a gidan mai sukai wa yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel