Siyasar Najeriya
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim, ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da jiga-jigan 'yan adawa a Ebonyi.
Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP ya kara samun nasara a karar da LP da ɗan takararta na gwamna suka nemi kotun ɗaukaka kara ta tsige shi, alkali ya kori karar.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce za a ga sabon tambarim NNPP a takardun kaɗa kuri'a na zaɓen gwamnan jihar Ondo mai zuwa a 2024.
Tsohon mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaɓen Atiku Abubakar, Daniel Bwala ya ce ya jima da raba jaha da babbar jam'iyyar adawa watau PDP.
Jigon jam'iyyar APC a Kano, Dan Bilki Kwamanda ya yi martani kan kura-kuran da gwamnatin Bola Tinubu ke aikatawa a Najeriya inda ya ce zai samu matsala a zabe.
Daniel Bwala ya yi martani mai zafi ga Sanata Ali Ndume kan caccakar gwamnatin Bola Tinubu da yake yawan yi inda ya ce sanatan bai kai ya soki shugaban ba.
Yayin da ake tsakiyar taƙaddama kan sarautar Kano, Sanata Masud Doguwa ya sanar da cewa shi da magoya bayansa sun hakura da tafiyar APC, sun koma PDP a Kano.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yaba da hukuncin hana tura kason kananan hukumomo zuwa asusun jihohi, ya ce wannan ci gaba ne.
An kuma samun shugaban ƙaramar hukumar na rikok kwarya a jihar Ribas ya naɗa mataimaka sama da 300, hakan na zuwa ne bayan hukuncin kotun ƙolin Najeriya.
Siyasar Najeriya
Samu kari