Shugaban Majalisar Dattawa Ya Rantsar da Sabbin Sanatoci 3, Sunaye Sun Bayyana

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Rantsar da Sabbin Sanatoci 3, Sunaye Sun Bayyana

  • Majalisar dattawan Najeriya ta rantsar da sabbin sanatoci uku a zamanta na yau Talata, 13 ga watan Fabrairu, 2024 a birnin tarayya Abuja
  • Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci rantsar da sanatocin da misalin ƙarfe 11:41 na safe kuma daga bisani aka nuna musu wurin zamansu
  • Waɗanda aka rantsar sun haɗa da Sanatan Ebonyi ta Kudu, Sanatan Filato ta Arewa da kuma Sanatan Yobe ta Gabas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya jagoranci rantsar da sabbin zababbun Sanatoci uku a zaman majalisar na ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.

Sabbin sanatocin da suka karɓi ranstuwar kama aikin sun haɗa da Prince Pam Mwadkon (Action Democratic Party, Filato ta Arewa) da Farfesa Anthony Ani (APC, Ebonyi ta Kudu).

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa mutum 5 a manyan muƙamai a babban banki CBN, ya tura saƙo Majalisa

Majalisar dattawa ta yi sabbin sanatoci 3.
Akpabio Ya Rantsar da Sabbin Sanatoci Uku a Zaman Majalisar Dattawan Najeriya Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Sai kuma na ƙarshe shi ne Sanata Mustapha Musa wanda zai wakilci mazaɓar Yobe ta Gabas a inuwa jam'iyyar APC, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Magatakardar majalisar dattawa, Mista Chinedu Akubueze, ne ya ba su rantsuwar kama aiki da misalin karfe 11:41 na safiya.

Jim.kaɗan bayan haka kuma aka nuna musu kujerunsu a zauren majalisar kuma kowane ya je ya zauna, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Majalisar ta gana da hafsoshin tsaron kasa

Yayin wannan zaman, majalisar ta kuma yi ganawar sirri da hafsoshin tsaro saboda tabarbarewar tsaro a kasar nan.

Waɗanda suka halarci zaman sun hada da babban hafsan tsaro, Christopher Musa, hafsan sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja, hafsan sojin sama, Hassan Abubakar, da hafsan sojin ruwa, Emmanuel Ogalla.

Baya ga batun tsaro, ‘yan majalisar sun kuma nuna matuƙar damuwa kan yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

Sakamakon haka ministan kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana a gaban majalisar dattawa domin yi wa sanatocin ƙarin haske.

Kotu ta maida shugaban APC na Benue kan kujerarsa

A wani rahoton na daban dakataccen shugaban jam'iyyar APC na jihar Benue, Mista Austin Agada, ya yi nasarar komawa kan kujerarsa bayan hukuncin kotu.

Babbar kotun jihar Benuwai ta soke naɗin mukaddashin shugaban APC, kana ta maida Agada kujerarsa ta shugaban jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel