Wata Sabuwa: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Arewa, Ta Faɗi Sahihin Mai Kujerar

Wata Sabuwa: Kotu Ta Tsige Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Arewa, Ta Faɗi Sahihin Mai Kujerar

  • Dakataccen shugaban jam'iyyar APC na jihar Benue, Mista Austin Agada, ya yi nasarar komawa kan kujerarsa bayan hukuncin kotu
  • Babbar kotun jihar Benuwai ta soke naɗin mukaddashin shugaban APC, kana ta maida Agada kujerarsa ta shugaban jam'iyyar
  • Mai shari'a Ikpambese ya ce alkalin da ya dakatar da Agada ba ta da hurumin sauraron ƙarar, don haka za a sauya alƙali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Babbar kotun jihar Benue ta maida Mista Austin Agaada a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Benuwai.

Mai shari'a Maurice Ikpambese shi ne ya bada wannan umarni yayin yanke hukunci kan buƙatar soke umarcin cikin shari'a wanda ya dakatar da Agada daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

Kotun ta soke naɗin shugaban APC na Benue.
Kotu Ta Maida Agada a Matsayinsa na Shugaban APC Ta Jihar Benue Hoto: Official APC
Asali: Twitter

Bayan sauraron hujjojin lauyan Agada, J.J Usman (SAN), Mai shari’a Ikpambese ya janye dokar hana Agada bayyana kansa da aiki a matsayin shugaban jam’iyya na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya ce dogaro da doka ta 39 sashi na 3 a kundin dokokin babbar kotun Benuwai 2023, tsawon wa'adin umarnin wucin gadi shi ne mako ɗaya, Channels tv ta ruwaito.

Dogaro da wannan, Alkalin kotun ta yanke cewa tunda an bada umarnin dakatar da shugaban APC ranar 2 ga watan Fabrairu, 2024, tsawon lokacin ya ƙare.

Ya kuma kara da cewa Mai shari’a Lillian Tsumba, wanda ta hana Agada nuna kansa a matsayin shugaban APC ta jihar Benuwai, ba ta da hurumin bayar da umarnin wucin gadi.

A cewarsa, ba ta da hurumin haka ne saboda ba babban alkalin jihar ko wani alkali da ke sama da ita ne ya naɗata ta saurari shari'ar ba, in ji rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Bayan lashe zaɓe, ƴan majalisa sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokoki a jihar Arewa

Ina makomar sabon shugaban APC na riƙo da aka naɗa?

Mai shari’a Ikpambese ya kara da soke nadin Benjamin Omakolo a matsayin shugaban riko na jam’iyyar APC a jihar da duk wani nadin da aka yi daga ranar 2 ga Fabrairu, 2024.

Ya kuma bayyana cewa za a miƙa batun ƙarar ga alkalin da ya cancanci sauraronta a babbar kotun.

APC na shirin kwace mulki a jihar Edo

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta jaddada cewa lokaci ya yi da za ta ƙwato mulkin jihar Edo daga ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024.

Muƙaddashin shugaban APC na jihar, Jarret Tenebe, ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai ranar Litinin a sakateriya da ke Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel