Bayan Lashe Zaɓe, Ƴan Majalisa Sun Zaɓi Sabon Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

Bayan Lashe Zaɓe, Ƴan Majalisa Sun Zaɓi Sabon Shugaban Majalisar Dokoki a Jihar Arewa

  • Mambobin sun kuma zaɓen Yakubu Liman a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna bayan ya lashe karishen zaɓe ranar Asabar
  • Liman, wanda kotun ɗaukaka ƙara ta tsige daga kujerarsa kana ta umarci a sauya zaɓe a rumfuna 5, ya sake komawa karo na biyu a zaman ranar Jumu'a
  • Majalisar ta rantsar da shi tare da wasu mambobi uku da suka samu nasara a zaben da aka cika ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna da aka tsige kwanakin baya, Yusuf Liman ya sake komawa kan kujerarsa.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, ƴan majalisar sun sake zaɓen Honorabul Liman a matsayin shugaban majalisar dokokin.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Birnin tarayya Abuja na fuskantar babbar barazana, majalisar dattawa ta magantu

Shugaban majalisar dokokin jihar Kaduna, Yakubu Liman.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Koma Kan Kujerarsa Hoto: Yakubu Liman
Asali: Facebook

Wannan na zuwa ne bayan nasarar da ya samu zaɓen da aka ƙarisa ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu, 2024 a mazaɓarsa ta jihar Kaduna, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon zaɓen ya nuna Liman na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri’u 18,068, inda ya doke Solomon Katuka na jam’iyyar PDP, wanda ya samu kuri’u 17,404.

Bayan haka, ranar Laraba hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) rashen Kaduna ta gabatar da takardar shedar lashe zaben ga tsohon shugaban majalisar.

Sauran ‘yan majalisar jiha da suka karbi takardar shaidar cin zabe sun hada da Haruna Barnabas (APC, Chawai), Jesse Tanko (APC, Chikun), da Nura Likoro (PDP, Kudan).

Taya tsohon kakakin ya sake komawa kan muƙamin?

Sai dai jim kadan bayan rantsar da shi, mambobin suka haɗa baki babu mai adawa suka zabi Honorabul Liman a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ɗauki muhimmin mataki da nufin gyara yadda ake zaɓe a Najeriya

Hakan ta faru ne yayin zaman majsalisa, inda aka rantsar da Liman tare da wasu mambobi uku da suka yi nasara a zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake jawabi bayan komawa kujerarsa, Liman ya yabawa abokan aikinsa ƴan majalisar bisa goyon baya da kuma yardar da suka nuna masa.

Sabon shugaban majalisar ya kuma yi alkawarin hada kai da bangaren zartaswa na gwamnati domin ci gaban dimokradiyya da jihar.

The Cable ta ce kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tsige Liman daga kan muƙaminsa a watan Nuwamba, 2023. Ta umarci a canza zaɓe a rumfuna 5 a mazaɓarsa Maƙera.

Gwamna Bago ya sa baki a cafke masu zanga-zanga

A wani rahoton kuma Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bada umarnin sakin jagorar waɗanda suka yi zanga-zanga a Minna, Aisha Jibrin, da wasu mutum 24

Kwamishinar yaɗa labarai da dabaru ta jihar, Binta Mamman, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari kan abinda ya sa a kama su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel