Atiku Ya Raba Gari da Wani na Kusa da Shi, Ya Bayyana Dalilansa

Atiku Ya Raba Gari da Wani na Kusa da Shi, Ya Bayyana Dalilansa

  • Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya gargaɗi kafafen yada labarai da sauran jama’a da su daina bayyana Daniel Bwala a matsayin tsohon mai taimaka masa
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ya ci gaba da cewa Bwala kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa ne kawai a zaɓen 2023
  • A cewar wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na Atiku ya fitar, aikin Bwala na kakakin yaƙin neman zaɓen ya ƙare ne bayan kammala zaɓe, kuma ya kamata kafafen yaɗa labarai su daina kiransa a matsayin mai taimaka masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, ya ce Daniel Bwala tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa ne kawai a zaɓen 2023 ba mai taimaka masa ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana alfanun da aka samu sakamakon rufe rumbunan masu boye abinci

Hakan ya fito ne a wata sanarwa daga ofishin yaɗa labarai na tsohon mataimakin shugaban ƙasar a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu, inda ta ƙara da cewa babban lauyan bai taɓa zama hadimi ga Atiku ba, cewar rahoton The Nation.

Atiku ya raba gari da Bwala
Atiku ya bukaci a daina kiran Bwala a matsayin hadiminsa Hoto: @BwalaDaniel, @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya nesanta kansa da Bwala

A cewar sanarwar, an ɗauki Bwala ne a matsayin mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa, kuma ya riƙe muƙamin ne a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a 2023, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ofishin yaɗa labaran Atiku ya bayyana cewa buƙatar mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen ta zo ƙarshe bayan kammala zaɓe, kuma lauyan ya ci gaba da harkokinsa na rayuwa.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Don haka wannan ya zama sanarwa ga ƴan jarida da jama'a da su daina ayyana Bwala a matsayin tsohon hadimin Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta gama shiri, ta faɗi jiha 1 da zata ƙwace mulki daga hannun gwamnan PDP a 2024

"Muna kira ga jama'a da su gane, gabatar, da kuma ayyana Daniel ta hanyar sana'arsa da ƙawancensu na yanzu."

Me yasa Atiku ya raba gari da Bwala?

A ranar 10 ga watan Janairu, 2024, Bwala ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Bayan makonni biyu, an gan shi tare da shugaban ƙasar a Faransa, lamarin da ya janyo cece-kuce game da biyayyarsa ga jagoran na PDP.

Sai dai Bwala ya ce lokacin siyasa ya wuce, kuma lokaci ya yi na mulki, shi ya sa a shirye yake ya marawa gwamnatin Shugaba Tinubu baya.

Bwala Na Son Aiki da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai magana da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar, Daniel Bwala ya nuna sha'awar yin aiki tare da Shugaba Tinubu.

Bwala ya bayyana cewa zai yi matuƙar farin ciki idan ya samu muƙami a gwamnatin Tinubu domin bayar da tashi irin gudunmawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel