Kashim Shettima Ya Shilla Kasar Waje Don Shajja’a Super Eagles a Wasan Karshe Na Afcon 2023

Kashim Shettima Ya Shilla Kasar Waje Don Shajja’a Super Eagles a Wasan Karshe Na Afcon 2023

  • Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya bar shugaban kasa Bola Tinubu a fadarsa tare da shillawa waje don kallon wasan Najeriya da Cote d'Ivoire a wasan karshe na AFCON 2023
  • A baya an ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ne zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya domin shajja’a Super Eagles ta Najeriya a filin wasa
  • A yayin da yake barin Najeriya, Shettima ya ci gaba da cewa, duk yadda ta kaya, nasara ce ga Najeriya

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya tashi daga fadar shugaban kasa domin nuna magoya bayan Najeriya wajen shajja’a Super Eagles ta Najeriya a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na 2023 da Cote d'Ivoire mai masaukin baki a Abidjan.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

A baya dai an ruwaito cewa shugaba Tinubu na shirin zuwa kallon wasan Najeriya da makwabciyarta Cote d'Ivoire a kasar ta Afrika.

Kashim ya tafi taya 'yan Super Eagles wasa a Abidjan
AFCON: Kashim ya tafi shajja'a 'yan Super Eagles | Hoto: Super Eagles, Kashim Shettima
Asali: Twitter

Sai dai, daga baya fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban zai ci gaba da zama a kasar, kuma Shettima ne zai jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Abidjan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta yaya Najeriya ta zo wasan karshe na AFCON?

Idan baku manta ba, Najeriya ta buga wasa da kasar Afrika ta Kudu a makon da ya gabata, inda ta yi nasara a kanta tare da samun ansarar wucewa zuwa gaba a wasan.

Wannan haka yake ga Cote d'Ivoire da ta lallasa DR Congo a wasan da suka buga a makon da ya gabata.

A halin da ake ciki, za a buga wasan ne a daren yau Lahadi 11 ga watan Faburairu, inda daga karshe kasa daya za ta kafa tarin lashe kofin AFCON 2023.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

An rasa rigar Super Eagles a Kano

A bangare guda, 'yan Najeriya masu kishin kasa a jihar Kano sun shiga rudani yayin da rigunan kungiyar Super Eagles suka kare kaf a kasuwa gabanin wasan karshe na AFCON.

A rahoton da muke samu daga jihar, a halin yanzu wasu 'yan jihar na neman siyan rigar ruwa a jallo, amma hakan ya ci tura duba da yadda ta yi karanci a kasuwannin Kano.

Ya zuwa jiya Asabar 10 ga watan Faburairu, rigar da ake siyarwa N5000 ta koma N15,000 nan take baya ga wahalar samunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel