Dilolin Wiwi a Morocco Sun Kauracewa Siyarwa Isra'ila Kayan Hayaki Kan Gallazawa Falasdinawa

Dilolin Wiwi a Morocco Sun Kauracewa Siyarwa Isra'ila Kayan Hayaki Kan Gallazawa Falasdinawa

  • Isra’ila da ke harkallar wiwi sun nuna damuwa kan yadda kasar Moroko ta yanke huldar safara a tsakaninsu
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki tsakanin ‘yan Hamas da sojojin Isra’la masu daurin gindin Amurka
  • Yaki tsakanin Falasdinawa da Isra’ilawa ba samo asali ne a shekaru sama da 70 da suka wuce, har yanzu ana fafatawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Isra’ila - Dillalan tabar wiwi a Moroko sun kauracewa sayarwa dilolin Isra'ila kaya don nuna adawa da yakin da Yahudawa ke yi kan mazauna Gaza, a cewar wani rahoto da kafar yada labaran Isra'ila ta fitar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

Majiya ta habarta cewa, shafin yada labarai na Isra’ila, Mako ya ambato wasu dillalan kayan maye na kasar Isra’ila da ke korafi kan raguwar huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

'Yan kasuwar tabar wiwi sun yanke alaka da Isra'ila
'Yan kasuwar Moroko na wiwi sun yanke da dilolin Isra'ila
Asali: Getty Images

Kafar yada labaran ta kuma ruwaito wani dillalin wiwi dan kasar Morocco yana cewa, sun ki sayarwa Isra'ilawa kayansu ne saboda uzurawa Falasdinawa ‘yan Gaza.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake safarar miyagun kwayoyi a Moroko

A rahotannin da ke shigowa, an bayyana yadda jami’an Moroko ke barin ‘yan harkallar kwaya su ci karensu babu babbaka idan suka ba da cin hanci, Middle East Eye ta ruwaito.

Hakan na ba da damar fitar da tabar wiwi da sauran kayan hayaki zuwa kasashen duniya daban-daban, ciki har da Isra’ila da ke kusa da Gaza.

Hakazalika, an yi tsokaci kan yadda Isra’ilawa ke haba-haba da kayan wiwi na kasar Moroko kasancewarsa ya fi na kasashe da yawa da kyau da raha.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan damfara suka yi kutse a lambar wayar gwamnan APC, sun fara neman kudade

Yakin Gaza da Isra’ila

Idan baku manta ba, kasar Isra’ila ta shiga yaki da Falasdinawa ne tun a watan Oktoban 2023, inda duniya ke ci gaba da Allah wadai da abin da ke faruwa.

Kasashe da dama sun bayyana rashin goyon bayansu ga Isra’ila da yadda take ci gaba da kai ruwan bama-bamai kan bayin Allah a zirin Gaza.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kiraye-kirayen tsakaita wuta da kuma tabbatar da kai wa mazauna Gaza tallafin kayan abinci da magani.

An kashe babban jigon Hamas

A wani hari da Isra’ila ta kai kan mazauna Beirut ta kasar Lebanon, ta yi ikrarin cewa, hari ne kan daya daga cikin shugabannin kungiyar hamayyarta Hamas, BBC News ta ruwaito.

Mark Reveg, mai magana da yawun Isra’ila ya ce, mataimakin shugaban Hamas, Saleh Al-Arouri ya mutu a wani harin da jirgin Isra’ila ya kai kan shugabannin Hamas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel