Siyasar Najeriya
'Yan Najeriya sun soki 'yan majalisar wakilan Najeriya bayan sun zabge kashi hamsin cikin ɗari na jimillar albashinsu. Sun bukaci su rage alawus din da suka kwasa.
Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin Malam Uba Sani, ta nisanta kanta da bidiyon cin zarafin da aka yi wa Dan Bilki Kwamanda. An zane shi da bulala.
Bayan tsige Sanata Ali Ndume da majalisa ta yi a jiya Laraba, an nada shi sabon mukami na lura da kwamitin harkokin bude ido a Najeriya. Godswill Akpabio ne ya sanar
Gwamnonin jam'iyyar PDP sun samu matsaya kan rikicin siyasar jihar Rivers tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike. Sun goyi bayan Fubara.
Daya daga cikin manyan makusantan siyasa na Peter Obi a Labour Party, Isaac Balami ya koma jam'iyyar APC wadda ya bari gabanin zaɓen shugaban kasa a 2023.
Sanata Ifeanyi Ubah da wasu manyan kusoshin APC daga jihar Anambra sun gana a birnin tarayya Abuja, ana zargin sun fara shirin tunkarar babban zaɓen gwamna.
Bayan sauke shi daga muƙamin babban mai ladabtarwa a majalisar dattawa, jam'iyyar APC ta shawarci Sanata Ali Ndume ya tattara kayansa ya koma jam'iyyar adawa.
Hukuncin kotun ƙoli na ba kananan hukumomi ƴanci ya sa gwamnoni sun fara gaggawar shirya zaben kananan hukumomi a jihohinsu. Mun tattara maku su duka.
Rahotanni daga jihar Abia da ke Kudu maso Gabashin Najeriya sun bayyana cewa kwamishinar noma da takwaranta na ma'aikatar kimiyya da fasaha sun aje aiki.
Siyasar Najeriya
Samu kari