Ganduje Ya Shiga Babbar Matsala Yayin da Matasan APC Suka Ɓalle da Zanga-Zanga Kan Abu 1

Ganduje Ya Shiga Babbar Matsala Yayin da Matasan APC Suka Ɓalle da Zanga-Zanga Kan Abu 1

  • Awanni bayan kammala zaɓen fidda gwani, matasan APC a jihar Edo sun gudanar da zanga-zangar adawa da shugabannin jam'iyya
  • Sun yi kira ga uwar jam'iyya ta ƙasa karkashin Ganduje ta rushe kwamitin gudanarwa (SWC) na jihar wanda Jarret Tenebe ke shugabanta
  • Masu zanga-zangar sun kuma jinjinawa shugaban kwamitin zaben fidda gwani kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Matasan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo sun fantsama zanga-zangar lumana yau Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024.

Matasan sun yi wannan zanga-zanga ne kan abinda suka kira mulkin kama karya na kwamitin ayyukan APC na jihar Edo (SWC).

Matasan APC sun yi zanga-zanga a Edo.
Matasan jam’iyyar APC a jihar Edo sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyukan SWC Hoto: APC
Asali: Getty Images

Masu zanga-zangar sun yi kira ga uwar jam'iyyar APC ta ƙasa karƙashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ta rushe shugabancin jam'iyya na jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya samu matsala a APC yayin da tsohon kwamishina ya fice daga jam'iyyar, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, matasan sun buƙaci a rushe SWC domin zaman lafiya ya samu gindin zama a jam'iyyar kuma a tunkari abinda ke gaba.

Masu zanga-zanga sun jinjinawa gwamnan Imo

Sai dai matasan APC na jihar Edo sun jinjina tare da yabawa shugaban kwamitin zaben fidda ɗan takarar gwamna kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma.

Sun yabawa Uzodinma ne bisa ayyana wakilin mazaɓar Ovia a majalisar wakilan tarayya, Dennis Idahosa, a matsayin sahihin ɗan takarar gwamna a zaɓen jihar da ke tafe.

Legit Hausa ta fahimci cewa hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta tsaida ranar 21 ga watan Satumba, 2024 domin gudanar da zaɓen gwamna a jihar Edo.

Jihar na ɗaya daga cikin jihohin da zaɓensu ya fita daga cikin ranar babban zaɓen gama gari, rahoton jaridar Blueprint.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun nemi Tinubu ya yi murabus, sun fadi dalili

Amma an shiga ruɗani kan waye sahihin ɗan takarar da ya lashe zaɓen fidda gwanin APC sakamakon yadda mutum 3 suka ayyana kansu a matsayin masu nasara.

Me ya kawo karancin mai a Abuja?

A wani rahoton kuma Ƙarancin man fetur ya mamaye babban birnin tarayya Abuja yayin da aka wayi garin Litinin mafi akasarin gidajen mai a rufe.

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar direbobi NARTO ta dakatar da ayyukan manyan tankoki da ke dakon man fetur kan tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel